24 Yuli 2025 - 15:42
Source: ABNA24
Shugaban Tunisiya Ya Kalubalanci Mai Ba Trump Shawara Da Hotunan Yara Gaza + Bidiyo

A ganawar da ya yi da babban mai baiwa Donald Trump shawara a hukumance, shugaban kasar Tunusiya ya yi magana game da irin wahalhalun da al'ummar Palasdinu ke ciki, ya kuma yi kakkausar suka kan ingancin al'ummar duniya ta hanyar nuna hotuna masu sosa rai na yaran Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya aike da sako kwakkwaran matakinsa kan laifukan bil'adama da Amurka da Isra’ila ke aikatawa a kasar Falasdinu ta hanyar nuna hotuna masu ratsa zuciya na yaran Gaza a yayin ganawarsu da Mossad Boulos babban mai ba Donald Trump shawara kan yankin gabas ta tsakiya da Afirka.

A cikin wani faifan bidiyo da fadar shugaban kasar Tunisiya ta fitar, Saied ya nuna hotunan kananan yara Falasdinawa a Gaza da suka fake da cin kasa saboda tsabagen yunwa.

Da yake magana kan ɗayan hotunan, Kais Saied ya ce: "Ina tsammanin waɗannan hotunan ka san su ka saba da ganinsu ku." Yaro yana kuka yana cin kasa a yankin Falasdinawa da aka mamaye... A karni na 21 bai samu abin da zai ci ba kawai yana rike da damken kasa a hannunsa... Wani hoton yaron da ke gab da mutuwa saboda babu abin da zai ci.

Da yake jaddada cewa ba za a amince da wannan laifin na dan Adam ta kowace hanya ba, ya kara da cewa: Shin wannan shine halaccin kasashen duniya? Halaccin da ke kara rugujewa kowace rana? Me ake nufi da irin wannan bala'i a kan al'ummar Palastinu a kowace rana da kowace sa'a?

Shugaban kasar Tunusiya ya yi kira da a farkarwar lamirin duniya, yana mai karawa da cewa: lokaci ya yi da dan Adam zai dawo cikin hayyacinsa, tare da dakatar da wadannan laifuffuka kan al'ummar Palastinu. A yau, al’ummar ’yan Adam sun riga kungiyoyin al’ummomin duniya kuma sun fito fili suna yin Allah-wadai da wadannan bala’o’i.

Ofishin shugaban kasar Tunisiya ya kuma sanar da cewa, baya ga batun Falasdinu, an kuma tattauna batutuwan da suka hada da ta'addanci da kuma halin da ake ciki a yankin Larabawa yayin wannan taron. Said ya jaddada wajabcin warware matsalolin cikin gida na kasashen Larabawa da su kansu al'ummomin kasashen, ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba, ya kuma kara da cewa, kasar Tunisia na ci gaba da fadada hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare bisa moriya da bukatun al'ummarta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha