Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mataimakin ministan shari'a da harkokin kasa da kasa a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Kazem Gharibabadi ya sanar a jiya alhamis cewa Iran ta amince da ziyarar da tawagar kwararrun hukumar zata kai birnin Tehran cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa. Sai dai ba za su ziyarci cibiyoyin nukiliyar Iran ba.
Mataimakin ministan shari'a da harkokin kasa da kasa a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Kazem Gharibabadi ya sanar a ranar Alhamis cewa Iran ta amince da ziyarar da tawagar kwararrun hukumar za ta kai birnin Tehran cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa. Sai dai ba za su ziyarci cibiyoyin nukiliyar Iran ba.
A baya dai Seyyed Abbas Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya sanar da hakan, biyo bayan wuce gona da irin da Amurka da Isra’ila suke yi kan Iran, wanda rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, Rafael Grossi ya gabatar, cewa hadin gwiwar da Iran za ta yi da wannan kungiya ba za ta kasance kamar da.
Da yake mayar da martani ga wata tambaya daga jaridar Wall Street Journal game da kasancewar tawagar kwararrun hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya a Tehran, kakakin hukumar ta IAEA ya ce ba zai ce uffan ba kan labarin.
Sai dai kakakin hukumar ta IAEA ya ce babban daraktan hukumar ya jaddada wa dukkan bangarorin "bukatar cimma matsaya ta diflomasiyya bisa tabbatar da sa ido da hukumar ta yi."
A cewar jaridar Wall Street, a makon da ya gabata, ministocin harkokin wajen kasashen Turai sun shaidawa ministan harkokin wajen Iran cewa, idan Iran ta koma tattaunawa da Amurka da kuma yin hadin gwiwa da hukumar, to, za su iya dage shirin kakabawa Iran din takunkuman kasashen turai.
A baya Araghchi ya ce Amurkawa ne suka ci amanar diflomasiyya tare da kai wa Iran hari a tsakiyar tattaunawar. Ya jaddada cewa dole ne Amurkawa su ba da tabbacin cewa idan tattaunawar ta koma, ba za a sake kai wa kasar hari ba.
Faransa da Jamus da kuma Birtaniya a matsayin kasashe uku da ke cikin kungiyar JCPOA, sun yi barazanar cewa idan har ba a samu ci gaba kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya da Iran ba, za su sake kakabawa Iran takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a karshen watan Agusta.
Iran ta kuma yi barazanar cewa, a mayar da martani ga wannan yunkuri na kasashen yamma, akwai zabi, ciki har da ficewa daga cikin tsarin NPT.
Your Comment