Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei (a) ya jaddada cewa nan gaba za’a shaida ci gaban dakaru da na ilimi cikin sauri fiye da na baya, kuma za su ci gaba zuwa ga kololuwar daukaka.
An fitar da sako daga Jagoran juyin juya halin Musulunci a daidai lokacin da ake cika kwanaki arba'in da shahadar wasu gungun 'yan kasar Iran, kwararrun kwamandojin soji, da manyan masana kimiyyar nukiliya kamar haka.
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Ya Ku Al'ummar Iran Masu Girman Daraja
Yau ake cika kwanaki arba’in da shahadar wasu ‘yan kasarmu masoya da suka hada da fitattun kwamandojin soji da masana kimiyyar nukiliya. Wanda fasidar kuma mujrimar kungiyar 'yan sahayoniya wanda suke muggan makiya kuma makiya al'ummar Iran.
Babu shakka, rashin shugabanni irin su Shahidai Bagheri, Salami, Rashid, Hajizadeh, Shadmani, da sauran jami'an soja, da masana kimiyya irin su Shahidai Tehranchi da Abbasi, da sauransu, zai zamo wani kaya ne mai nauyi ga kowace al'umma.
Sai dai kuma wannan makiyin wawa mai gajeran hangen nesa bai cimma manufarsa ba. A Nan gaba za ta bayyana cewa yunkurin soja da na kimiyya za su ci gaba zuwa ga kololuwar daraja da sauri fiye da na baya, in Allah Ya yarda.
Shahidanmu sun zabi hanya mai cike da fatan samun daukakar matsayi na shahada, daga karshe kuma sun cimma abin da dukkan masu sadaukarwa suke so, Allah ya yi musu rahama. Sai dai kuma bakin cikin da saukawar al'ummar Iran musamman iyalan shahidai musamman ma wadanda suka san su na kusa, mai tsanani ne da daci da nauyi.
A Cikin Wannan Lamarin, Akwai Bangarori Da Yawa Masu Haske Waɗanda Suke Bayyana A Fili:
Na farko dai tsayin daka da hakuri da kyawawan halaye na wadanda suka tsira, wadanda ba a iya ganin irinsu ba sa a ci gaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Na biyu tsayin daka da tsayin daka na cibiyoyi da shahidai ke jagoranta, wadanda ba su bari wannan mummunan rauni ya hana su yunkurin dama ta gaba ba ko ya gurgunta yunkurinsu ba.
Na uku, daukakar tsayin daka mai ban mamaki na al'ummar Iran, wanda ya bayyana cikin hadin kai, karfin ruhi, da azamar dagewa a fagen fama. Iran din musulunci ta sake nuna irin kafuwarta a wannan lamari. Makiya Iran suna kai farmaki ne kan karfe mai sanyi.
Iran din Musulunci za ta kara karfi a kowace rana in Allah ya yarda. Yana da mahimmanci kada a manta da wannan hakikar gaskiyar da ayyukan da ta kunsa. Kiyaye hadin kan kasa ya zama wajibi ga kowannenmu.
Haɓakawar da a ke bukata wajen ci gaban ilimi da fasaha a kowane fanni wajibi ne ga manyan masana kimiyya. Kiyaye martaba kasa da martabar al'umma aiki ne da ba ya karewa ga masu magana da marubuta.
Samarwa da kasa hanyoyin da za ta kara tabbatar da tsaronta da 'yancin kai wani aiki ne na kwamandojin soji. Tsanani da sa ido kan ayyukan kasa da nasarorin da aka samu wani nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan hukumomin zartaswa da ke da alhakin hakan.
Bayar da shiriya ta ruhi, da haskaka zukata, da nasiha ga mutane da su kasance masu haquri, da natsuwa, da tsayin daka, wajibi ne a kan malamai. Kiyaye kishi da wayar da kan jama'a ya zama wajibi a kan mu baki daya musamman matasa. Allah ya ba kowa nasara.
Amincin Allah ya tabbata ga al'ummar Iran, tsira da amincin Allah su tabbata ga matasa shahidai, mata da yara shahidai, da dukkan shahidai da iyalansu.
Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Sayyid Ali Khamenei
25 ga Yuli, 2025
Your Comment