26 Yuli 2025 - 23:48
Source: ABNA24
Najeriya: An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Don Tunawa Da Waki'ar 25 July Karo Na 11 A Abuja + Hotuna

Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta gudanar da taron Tunawa da waki'ar 25july tasu Shahid Ahmad, Hameed, Mahmud, da sauran shahidai 31 karo na 11 a Abuja

Taron wanda ya samu halartar yan'uwa da al'ummar gari, wanda aka gabatar da jawabai da dama, akan maudu'eh mabanbanta, cikin masu jawabi hadda bakin da aka haska jawabansu daga ketaren kasa, sannan Malama Zeenah Ibrahim ta gabatar da jawabi.

Taron ya gudana ne a wani babban dakin taro dake Birnin Tarayya Abuja

Takaitaccen Bayani

Shekaru Sha Ɗaya (11) Da Gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan Ya Kashe Ƴan Uwanmu Mutum (34).

Yau Juma'a 25/July/2025, Shekaru 11 da Kashe wa Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ƴaƴa 3 Tare da Almajiran sa Mutum 30

A ranar 25-Jul-2014 Sojojin Najeriya suka Afkawa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da kira a garin Zaria cikin watan Ramadan a lokacin da suka fito Muzaharar nuna goyon baya ga Falasɗinu, kin amincewa da kashe Al'ummar kasar Palestine da Isra'ila ke yi tsawon Shekaru masu yawa da kuma bayyanawa duniya cewa Masallacin Qudus na Musulmi ne. A Lissafi na watannin Miladiyya yau ake cika shekaru 11 cur da wannan ta'addanci, wanda a watannin Hijiriyyah kuma ya faru ne a ranar 28 ga watan Ramadan.

A ranar sun kashe mutane 34 ciki Har da 'Ya'yan Jagora Sayyid Zakzaky (H) guda Uku, Shaheed Ahmad, Shaheed Hameed, Shaheed Mahmud.

Azzalumai sun kashe masa Yaya da tunanin zai canza daga yadda yake, Zai samu rauni a zuciya, Zai tsorata yayi Surrender, Amma ranar 28-Jul-2014 kawai sai aka ga sheikh Zakzaky(h) Cikin Kwarin Gwuiwa yana sallatar Gâwár Yayansa da sauran mutane 31. Abin mamakin da kansa ya sakasu cikin Kabarin su, Sai babban Ɗansa Muhammmad da ya riƙa taimaka masa.

Lallai wannan abun da Sayyid Elzakzaky (H) ya yi, Ya gogewa Azzalumai hadda, Kai har da sauran mutane ma. Janothan bamu manta ba, Bamu Yafe ba, Zamu rama Insha Allah.

Jinjina ga dukkanin Shahidanmu na Ranar Qudus, 24 July 2014.

 Allah ya Ƙara Girmama Matsayin Shuhada'u Maula Abba, ya ƙara tabbatar damu akan tafarkin da suka bari Ya Ilaheey Ya bamu matsayi irin Nasu.

Marubuta:

Isa Charis

AliSajjad Taheer

Shaheedah Bintu Basheer

Fi'amanillah Ya Shuhada'u

30/1447AlMuharram

25/July/2025

Your Comment

You are replying to: .
captcha