26 Yuli 2025 - 14:45
Source: Quds
Mutane 127 Da Suka Hada Da Yara 85 Ne Suka Mutu Sakamakon Yunwa A Gaza

A cewar sanarwar a hukumance na cibiyar kula da lafiya ta Shifa, cibiyar kula da lafiya mafi girma a zirin Gaza, mutane biyar da suka hada da yara biyu sun mutu sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki a cikin sa'o'i 24 da suka gabata kadai.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – bisa nakaltowa daga kamfanin labaran Qudus ya habarta cewa: Daraktan cibiyar Shifa ya sanar a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa: "A cikin sa'o'i 24 da suka gabata an sami labarin shahadar Falasdinawa 5 da suka hada da yara biyu saboda karancin abinci da kuma tabarbarewar yanayin abinci".

Ya kuma sanar da cewa adadin shahidai 127 ne aka tabbatar sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankin Zirin Gaza, inda ya kara da cewa: "A cikin wannan adadi 85 yara ne, yara da raunin jikinsu ya kasa jurewa wannan bala'i na dan Adam".

An buga wannan muguwar kididdigar a daidai lokacin da manyan yankunan Zirin Gaza ke fuskantar karancin abinci, ruwan sha, magunguna, da kuma ababen more rayuwa saboda tsananin kawanya da lalata kayayyakin kiwon lafiya da na agaji da Isra’ila ke yi aiwatarwa a Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha