Masar Ta Yi Amai Ta Lashe Dangane Da Kiran Kai Dauki Wa Gaza

Sheikh Al-Azhar Yayi Kira Da A Ceto Gaza Daga Mutuwa

Masar Matsa Namba Kan Sheikh Al-Azhar Don Janye Maganar Da Yayi Kan Yunwa A Gaza
23 Yuli 2025 - 12:01
Source: Quds
Sheikh Al-Azhar Yayi Kira Da A Ceto Gaza Daga Mutuwa

A cikin wani sako da ya fitar, Sheikh Al-Azhar ya yi kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin ceto rayukan mazauna yankin Zirin Gaza daga yunwa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa:  A cikin wani sako da ya aike, Sheikh Ahmed Al-Tayeb ya bayyana cewa: Dangane da ci gaba da kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa mazauna zirin Gaza, ana jarabta tunanin dan Adam ne, kuma masu goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan ta fuskar makamai da siyasa, abokan hulda ne kai tsaye kan wadannan laifuka.

Tare da kuka mai cike da bakin ciki da kuka mai zubar da jini, muna kira ga lamiri masu 'yanci, masu hikima da ilimi na duniya da su kubutar da mazauna Zirin Gaza daga mummunan zalunci, da ba a taba ganin irinsa ba na yunwa da gwamnatin Sahayoniya ta ke aiwatarwa a Gaza.

Masar Matsa Namba Kan Sheikh Al-Azhar Don Janye Maganar Da Yayi Kan Yunwa A Gaza

Kamfanin dillancin labaran Al Arabi Al-Jadeed ya habarta cewa: daga majiya mai tushe cewa, an tilastawa Ahmed Al-Tayeb, shehin Al-Azhar domin ya goge wata sanarwa da ya fitar dangane da bala'in jin kai da ke faruwa Gaza da kuma laifukan da gwamnatin sahyoniyawa ta yi kan fararen hula a karkashin matsin lamba daga manyan hukumomi a gwamnatin Masar.

A cewar wadannan majiyoyin, an yi la'akari da wannan magana da ta ci karo da manufofin diflomasiyya na gwamnatin Masar a halin yanzu, lamarin da ya sa manyan jami'an kasar suka mayar da martani cikin gaggawa.

Tun da farko dai an buga wannan sanarwa a kafafen yada labarai daban-daban da suka hada da kafafan yada labarai da ke da alaka da hukumomin tsaron Masar, amma jim kadan bayan haka aka fitar da sanarwar daga kafafen yada labarai ta hanyar ba da umarni kai tsaye daga Jami’ar Azhar, inda suka ce ana sake bitarta sanarwar da gyara ta; lamarin da ba’a sake buga sanarwar ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha