Bidiyon Yadda Iran Ta Kori Jirgin Dakon Kayan Amurka Daga Yankin Takun Ta

Bidiyon Yadda Akai Musayar Canje Tsakanin Tsakanin Jirgin Saman Iran Da Jirgin Dakon Kaya Na Amurka
23 Yuli 2025 - 19:06
Source: ABNA24
Bidiyon Yadda Iran Ta Kori Jirgin Dakon Kayan Amurka Daga Yankin Takun Ta

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na dakarun ruwan Iran ya gargadi wani jirgin ruwan Amurka inda ya hana shi shiga yankin ruwan Iran.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: a ranar Laraba 23 ga watan yuni shekarar 2025 da misalin karfe 10 na safe, wani jirgin ruwa na Amurka mai suna DDG Fitzgerald ya yi niyyar tunkarar yankin ruwan da ke karkashin kulawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cewar Tasnim, Tawagar Rundunar Sojin Ruwa da dakarun tsaron Saman taku na yanki na uku na Nubuwwat (Nadaja) sun yi ta tashi ta jirgin helikwafta cikin gaggawa tare da yin shawagi a kan wannan jirgin da ya shiga yankin tare da ba da gargadin cewa yayi nesa tare da canja hanya.

Sai dai a martanin da jirgin na Amurkan ya yi barazanar kai wa jirgin Iran mai saukar ungulu hari ya kuma bukaci ya bar yankin. Sai dai matukin jirgin na Iran ya ci gaba da aikinsa da azama tare da sake maimaita gargadin kauracewa ruwan Iran.

Dangane da wannan sabuwar barazanar harbin daga jirgin Amurka, maa’aikatan tsarin tsaron sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fara aiki tare da fitar da wani sako mai inganci cewa jirgin helikwaftan ruwan yana karkashin cikakken kariyar tsaro da zai iya kare kansa daga duk wani barazana, tare da cewa jirgin Amurka ya wajaba ya canza hanyarsa zuwa kudanci.

Tare da dagewar tawagar jirgin da kuma goyon bayan tsaron da sojojin Iran suke samu, daga karshe ma'aikacin jirgin Amurka mai cike da kayan aiki ya mika wuya tare da kaurace wa shiga yankin ruwan da ke karkashin kulawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Your Comment

You are replying to: .
captcha