Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Mataimakin shugaban tawagar yada labaran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, yayin da yake ishara da mummunan halin jin kai a zirin Gaza ya sanar da cewa: Al'ummar Gaza na mutuwa da yunwa, kuma ba a taba ganin irin wannan yanayin ba a wani waje a duniya.
Ya kara da cewa: Mun yi iya kokarinmu don taimakawa al'ummar Palasdinu, amma har yanzu muna jin kunyar abin da muke iyawa, don haka muna neman fadada ayyukan soji da muke yi kan makiya yahudawan sahyoniya.
Manazarcin Yaman: Ayyukan Yaman Sun Zama Kaya A Gwamnatin Sahayoniya
Masanin siyasar kasar Yemen Abdul Ghani Al-Zubaidi, a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Masirah ya ce: Ayyukan sojojin Yemen da yan gwagwarmaya sun takura gwamnatin sahyoniyawa ba kawai ta fannin soji ba, har ma ta fuskar tunani da kuma hanyoyin sadarwa.
Al-Zubaidi ya jaddada cewa: Wannan tsari sako ne karara na matsayin kasar Yemen da al'ummar Palastinu. Hare-haren da Yaman suka kai kan jiragen ruwa na Isra'ila a cikin tekun Bahar Rum ya jawo wa wannan gwamnati tsadar tattalin arziki da tunani.
Wadannan hare-haren sun kusan kawo cikas ga dabarun soja da na kasuwancin Tel Aviv tare da nuna irin tasirin da Yemen ke da shi.
Your Comment