22 Yuli 2025 - 19:04
Source: ABNA24
Jiragen Saman Yaman Sun Kai Hari A Yankunan Da Aka Mamaye Ba Tare Da Gargadi Ba

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ba da rahoton wani hari da jiragen yaki mara matuki daga kasar Yemen suka kai kan yankunan da Isra’ila ta mamaye ba tare da gargadi ba

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - ya habarta cewa: Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton wani hari da jiragen yaki mara matuki daga kasar Yemen suka kai kan yankunan da Isra’ila ta mamaye’ inda Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, an harba wani jirgi mara matuki daga yankin Yaman zuwa yankunan mamaya.

An kai harin ne a daidai lokacin da babu daya daga cikin na'urorin gargadi da suka kada a yankunan da aka mamaye. Jami'an sojin Isra'ila sun bayyana damuwa game da rashin aiki na tsarin gargadin.

Isra'ila dai ta sha fama da hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuka daga dakarun Yaman a 'yan watannin nan. Hare-haren da kungiyar Ansarullah ta Yaman ke kai wa ya yi kamari, musamman bayan da aka fara yakin Gaza, tare da kai hare-hare a wurare kamar tashar jiragen ruwa na Eilat.

Your Comment

You are replying to: .
captcha