Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: A wani binciken kuma an tabbatar da cewa sabon salon tsarin bari kayan agaji da gwamnatin Sahayoniya ta bari an tsara shi ne don raba mazauna Gaza daga gidajensu ne.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Euro-Mediterranean ta sanar da cewa: Sabon tsarin agajin da gwamnatin sahyoniyawan ta bari akai a Gaza ya saba wa dokokin kasa da kasa kuma an tsara shi ne don raba mazauna Gaza da kuma karfafa mulkin soja.
Manufar tsarin agajin da gwamnatin sahyoniyawa ta bari akai na da nufin yaudarar ra'ayoyin jama'a na duniya ne kawai domin suga kamar ana kai kayan da gaske ne, wanda a baya-bayan nan ya mayar da hankali kan mummunan halin jin kai a Gaza.
Bisa ga hangen ƙungiyarmu, yana da wuya a iya biyan bukatun yau da kullum ta hanyar ƙuntatawa da tsarin tsari wanda ikon mamayewa ke sarrafawa.
Cibiyoyin rarraba agaji guda hudu da sojojin Isra'ila suka kafa ba za su iya biyan bukatun jama'a cikin aminci ko kuma yadda ya kamata ba.
Your Comment