ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Ali-Reza wahhab-zade yana fadar haka a ranar Lahadi, ya kuma kara da cewa za’a gudanar da marhala ta biyu na gwajin ne a kan mutane a kasar ta Cuba.
Wahhab Zade ya kara da cewa idan an kammala ayyukan gwaje –gwajen cikin nasara za’a fara samar da alluran riga kafin ne a cikin kasar Iran.
Cutar Covid 19 dai ta bulla ne a birnin Wuhan na kasar Sin a karshen shekara ta 2019, sannan ya zuwa yanzu ta kama mutane fiye da miliyon 90, a yayinda mutane fiye da miliyon daya da dubu 900 suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar a duniya.
342/