ABNA24 : Wa’izy wanda ya gana da mataimakin pira ministan kasar Azerbaijan ya ci gaba da cewa; Iran ta yi imani da cewa wajibi ne a samo hanyar warware sabanin dake tsakanin kasashe, musamman masu makwabtaka da juna ta hanyar diplomasiyya ba ta yaki ba.
Har ila yau, Mahmud Wa’izy ya ce; Yin taruka da za su kunshi Iran, Rasha, Azerbaijan, Turkiya da Armenia za su taimaka wajen kusantar juna da kuma ci gaban tattalin arziki.
A nashi gefen, mataimakin Pira ministan kasar ta Azerbaijan, ya sanar da cewa; shugaban kasarsu Ilham Alivey, ya yi imani da cewa ya kamata a ce iyakar kasashen biyu ta zama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Har ila yau ya kara da cewa; Shugaban kasar ta Azerbaijan yana yin jinjina da godiya ga jamhuriyar Musulunci ta Iran da jagororinta akan matsayar da suka dauka dangane da sabani da kasar Armenia.
342/