ABNA24 : Gwamnatin Somaliya dai ta zargi kasar Kenya da tsoma baki a harkokin siyasar kasarta.
Dama dai a alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade tana samun tangarda, inda a wata daya da ya gabata Somaliyan ta kira yi jakadanta daga Nairobi, tare da korar jakadan Kenya daga Magadishu.
Zargin da Somalia take yi wa Kenya, y akunshi tsoma baki a harkokin zaben da aka gudanar a yankin Jubaland wanda daya ne daga cikin yankunan Kasar Somaliya 5 masu kwarya-kwarya cin gashin kai.
A shekaru baya, kasar Kenya ta aike da sojoji zuwa cikin kasar Somalia domin yakar kungiyar Al-Shabab, sai dai ba a je ko’ina ta janye su bayan wani mummunan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan sojojin nata.
Har ila yau kungiyar ta Al-Shabab ta rika kai hare-hare a cikin kasar Kenya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa, a cikin cibiyoyin kasuwanci da kuma na ilimi.
342/