2 Disamba 2020 - 13:26
Iraki:Sojoji Da Dakarun Hashdu Sun Gudanar Da Ayyukan Tsaro Na Hadin Guiwa A Lardin Ambar

Majiyar dakarun Hashdushabi ta kasar Iraki ta bada sanarwan cewa ta gudanar da ayyukan tsaro na hadin guiwa da sojojin kasar a Lardin Ambar don zakulo ragowar mayakan Daesh a lardin a jiya Talata.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanin da dakarun suka fitar a jiya Talata da yamma yana cewa ayyukan tsaron an aiwatar da su ne a yankunan Sad-Madisis, Wadi Addiya, Alkaarah, Bunyanu-Sahil, da kuma Almanakh. Labarin ya kara da cewa ayyukan sun hada da bincike don gano mabuyar yan ta’adda na kungiyar Daesh a wadannan wuare. 

342/