ABNA24 : Shugaba Rouhanin ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da sarkin Qatar Sheikh Tanim bin Hamad al Thani inda ya ce wajibi ne kasashen yankin su kawo karshen siyasar dogaro da kasashen waje sannan su dawo ga tafarkin tatttaunawa a tsakaninsu don magance matsalolin da ke tsakaninsu.
Shugaba Rouhani ya ce abin cikin shi ne cewa shigo da gwamnatin sahyoniyawa cikin lamurran da suka shafi yankin nan babu abin da zai haifar in ban da rashin tsaro ga yankin, don haka shugaba Rouhanin ya bayyana mamakinsa ga yadda wasu kasashen yankin suka jingina tsaron kansu ga kulla alaka da haramtacciyar gwamnatin Sahyoniyawa, wacce abokiyar gabar dukkanin kasashen yankin da kuma sauran kasashen musulmi ne inji shugaban na Iran.
Har ila yau shugaban na Iran ya ce kasashen yankin za su iya magance dukkanin matsalolin da suke fuskanta ta hanyar tattaunawa a tsakaninsu a matsayinsu na makwabta, don haka yayi fatan cewa abubuwan da suke faruwa a yankin da ma duniya baki daya za su sanya kasashen yankin su hada kansu waje guda don ciyar da kasashen su gaba.
Shi ma a nasa bangaren Sarkin na Qatar, Sheikh Tanim bin Hamad al Thani, ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda alakar da ke tsakanin kasashen biyu take kara karfafa yana mai cewa kasarsa za ta ci gaba da kokari wajen ganin wannan alakar ta kara karfafa, kamar yadda kuma ya gayyaci shugaban na Iran da ya kawo ziyara kasar Qatar lamarin da shugaba Rouhanin ya amsa da kuma cewa yana fatan hakan za ta faru cikin lokaci.
342/