23 Nuwamba 2020 - 17:40
Sabuwar Tankar Yakin “ Karrar” Da Iran Ta Kera Tana Cikin Gwaji Na Karshe

Kwamandan sojan kasa na Iran Birgediya Janar Kioumars Haidari ya bayyana cewa; Tankar yaki kirar Iran da aka bai wa sunan “ Karrar” tana cikin gwaji na karshe gabanin a mika ta ga sojojin kasar.

ABNA24 : Haidari ya kara da cewa; A matsayina na kwamanda ina da masaniya akan cewa an mika wa banagren da ke kula da Tankokin yaki na soja, sabuwar takar Karrar, domin yin gwaji da kuma tantance ta gabanin sojoji su fara amfani da ita.

Kwamandan ya kara da cewa; Idan Tankar ta tsallake gwajin da ake yi ma ta za a mika wa sojojin kasa irinta mai yawan gaske.

Tsohon ministan tsaron Iran Birgadiya Janar Husain Dehqan, ya bayyana tankar ta Karrar da cewa; Tana cikin mafi karfi kuma kai dauke da kayan aiki na zamani a duniya.”

342/