13 Nuwamba 2020 - 14:26
Habasha:Jarigen Yakin Kasar Sun Yi Luguden Wuta Kan Rumbunan Makamai Na Yankin Tigray

Majiyar sojojin kasar Habasha ta bada sanarwan cewa jiragen saman yakin kasar sun lalata makamai da dama a rumbunan ajiyar makamai na kungiyar kwatar ‘yencin yan kabilar Tigray a yankin nasu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce, a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne firai ministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed, ya bawa sojojin kasar umurnin kwace iko da yankin Tigray daga hannun kungiyar yan tawayen na ‘Tigray Liberation Army’.

Ya zuwa yanzu dai an kashe daruruwan mutane a bangarorin biyu sannan mutanen da dama sun tsallaka kan iyakar kasar da kasar Sudan don neman mafaka.

Kafin haka dai yan kabilar Tigray ne suka rike da madafun iko a kasar, amma bayan zuwan Abiy Ahmed kan kujerar firaiministan kasar a shekara ta 2018, al-amura suka canza, wanda kuma ya kai ga mutanen yankin Tigray suke neman bellewa daga kasar.(19)

342/