30 Satumba 2026 - 18:05
Source: ABNA24
Ficewar Amurka Daga Iraki; Samun Babban Canji A Muhallin Tsaro Na Yammacin Asiya + Bidiyo

Sojojin Amurka na ƙarshe da "haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa" tare da ficewarsu daga Iraki, sun kawo ƙarshen fiye da shekaru ashirin na kasancewar sojin Washington a wannan ƙasar wanda ya bayar da sakamakon rashin aminci ga yankin; canjin da tare da tattaunawar da ake yi kan rage kasancewar sojin Amurka a yankin tekun Farisa, zai iya zama alama ta canji a salon kasancewar Washington a yammacin Asiya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Gungun Sojojin Amurka na ƙarshe bayan shekaru 23 na kasancewar soji, sun bar Iraki kuma abin da ake kira aikin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa ƙarƙashin jagorancin Amurka a wannan ƙasar ya kawo ƙare.

An gudanar da wannan ficewa ne bisa yarjejeniyar Baghdad da Washington a shekarar 2024. Dangane da wannan yarjejeniya, aikin soji na haɗin gwiwar zai ƙare har zuwa 30 ga Satumba 2026 sannan bayan haka dangantakar Baghdad da ƙasashe mambobin haɗin gwiwar za ta ci gaba a wasu tsare-tsare.

Daga Harin 2003 Har Zuwa Ficewar 2026

Kasancewar sojin Amurka a Iraki ya fara ne daga harin shekarar 2003. Sojojin Amurka bayan hambarar da gwamnatin Saddam, sun ci gaba da zama a Iraki shekaru da yawa kuma a wani mataki adadinsu ya kai fiye da mutum 170,000.

Amurka a shekarar 2011 ta fitar da sojojinta daga Iraki, amma da ƙirƙira da bayyanar Da'ish a shekarar 2014 ta sake samar da dalilin komawarta a cikin abin da aka kira haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa kan Da'ish.

Bayan ƙarshen mulkin Da'ish da rugujewar tsarin wannan ƙungiyar ta'addanci, aikin sojojin haɗin gwiwar ya canza daga ayyukan yaƙi zuwa horoswa, shawara da tallafi kuma a ƙarshe Baghdad da Washington a shekarar 2024 sun cimma yarjejeniya kan kawo ƙarshen kasancewar sojin haɗin gwiwar.

Yanzu, bayan fiye da shekaru ashirin, sojojin Amurka ba za su ƙara kasancewa a Iraki ba.

Ƙarshen Kasancewar Soji Da Bai Haifar Wa Yankin Komai Ba Sai Rashin Aminci Da Tsaro

Ficewar sojojin Amurka na ƙarshe daga Iraki yana faruwa ne a yanayin da fiye da shekaru ashirin da suka wuce tun shigowar sojin Amurka cikin wannan ƙasar; shekaru ashirin da suka fara mamayar Iraki a shekarar 2003, sun bar kusan mutum miliyan ɗaya da aka kashe kuma sun jefa wannan ƙasar cikin shekaru na yaƙi, ta'addanci, rashin kwanciyar hankalin siyasa da lalata ababen more rayuwa. Yanzu wannan ƙarfin Soji da ya shiga Iraki da taken samar da aminci da kwanciyar hankali, yana barin sansanoninsa na ƙarshe.

Abin da ya rage daga Iraki, ba ƙididdigar ficewar dubban sojojin Amurka kawai ba ne. Harin 2003 ya rushe tsarin siyasa da tsaro na Iraki kuma ya haifar da shekaru na tashin hankalin ƙungiyoyi da ta'addanci. Binciken da aka wallafa a matakai daban-daban, sun ba da labarin ƙaruwar mace-mace mai tsanani a Iraki bayan harin da ɗaruruwan dubban ƙarin mace-mace; binciken da suka biyo baya ma sun nanata girman asarar rayuka na yaƙin.

Ko bayyanar Da'ish ba za a iya raba ta da hargitsin da ya samo asali bayan mamayar Iraki ba. A cikin irin wannan yanayi, Amurka da farko ta shiga da yaƙi, sannan don tunkarar sakamakon wannan rashin kwanciyar hankalin ta sake komawa yankin kuma ta ci gaba da kasancewar sojinta shekaru da yawa.

Yaƙin Kwanan Nan; Ƙarshen Wurin Aminci Ga Sansanonin Amurka

Amma ficewar Amurkawa daga Iraki bai faru a haka nan kawai ba wanda ya zamo yaƙin Amurka da Iran na kwanan nan ana iya ɗaukarsa ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka canza lissafin soji na Washington a yammacin Asiya.

Hare-haren Iran kan sansanoni da wuraren Amurka a yankin, sun yi mummunar barna ga ababen more rayuwar sojin wannan ƙasar. Dangane da rahoton manyan majiyoyin watsa labarai na Amurka ciki har da Washington Post, Pentagon bayan waɗannan hare-haren, ta nazarci rage kasancewar sojin Amurka a ynakin tekun Farisa kuma har ma an gabatar da shakku kan gaza sake gina wasu sansanonin da aka lalata da wannan ƙarfin da suka kasance da shi a baya.

Wannan lamari yana da muhimmanci ta wani fanni: babban ɓangare na dabarun Amurka a yankin ya dogara ne kan cibiyar sansanonin soji, sojojin da aka tura da wuraren kayan aiki; amma yaƙin kwanan nan ya nuna waɗannan sansanonin, sabanin tunanin da, ba su da kariya daga hari kuma kiyaye su na iya haifar wa Washington asara masu nauyi. Dangane da haka yawancin masu nazari suna ɗaukar hare-haren Iran a matsayin alama ta mummunan rauni na wannan salon kasancewar soji.

Yankin Bai Zamo Kamar Na 2003 Ba Ne

A cikin irin wannan yanayi, ficewar Amurka daga Iraki ya kamata a kalle shi a matsayin wani ɓangare na babban canji a muhallin tsaro na yammacin Asiya. Amurka har yanzu tana nan a yankin kuma ficewa daga Iraki ba ya nufin ƙarshen tasirin siyasa da soji na Washington; amma salon kasancewa kai tsaye da yawa da ya samo asali bayan mamayar Iraki, ya fuskanci cikasa mai tsanani.

Ƙasashen yankin ma a yanzu sun fi fahimtar hakan sama da a cikin shekarun da suka gabata cewa dogaro kan kasancewar sojin manyan ƙarfin waje ba lalle yana iya samar da aminci mai ɗorewa ba. Yaƙe-yaƙen Iraki da Afghanistan, rikice-rikicen Siriya da Yemen da ci gaba da tashin hankalin yankin, tare da gogewar yaƙin kwanan nan, sun ƙara bayyana girmana asarar wannan salon.

Saboda haka, ficewar Amurka daga Iraki ba motsin sojoji kawai ba ne. Wannan ficewar tana faruwa ne a yanayin da tasirin shekaru ashirin na kasancewar sojin Amurka a Iraki ya haɗa da yaƙi, asarar rayuka da rashin kwanciyar hankali kuma a lokaci guda, ikon Amurka na kiyaye cibiyar sansanoninta a yankin ya fuskanci sabbin ƙalubale.

Amurka tana barin Iraki; amma abin da ke da muhimmanci bayan wannan ficewa, ba ƙarshen wani aikin soji kawai ba ne. Babban batu shi ne cewa salon kasancewar sojin Amurka kai tsaye a yammacin Asiya, bayan fiye da shekaru ashirin na yaƙi da rikici, ya fuskanci ƙaruwar asara da matsi da sabbin tabarbarewa. Ficewa daga Iraki a cikin irin wannan yanayi na iya zama ɗaya daga cikin alamun canjin ma'auni da yaƙin kwanan nan ya ƙara saurinsa aukuwarsa.

.........................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha