ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto jam’iyyar tana fadar haka a wani bayanin da ta fitar a yau Lahadi, a bikin cika shekaru 19 da kafa jam’iyyar.
Bayanin ya kara da cewa manufar kafa jam’iyyar ita ce tabbatar da cewa mutanen kasar suna da damar shiga cikin harkokin siyasar kasarsu, su kuma fayyace makomarsu da kansu.
An kafa jam’iyyar Wafiq ta kasar Bahrain ne a shekara ta 2001. Kuma Sheikh Ali Salman ne shugabanta, wanda a halin yanzu yake tsare a gidan yarin Sarakunan na Ali Khalifa a birnin Manama babban birnin kasar.
Tun shekara ta 2011 mutanen kasar Bahrai karkashin jam’iyyar Wifaq suka fara yunkurin neman a basu damar shiga cikin harkokin siyasar kasar, amma gwamnatin Ali Khalifa tare da taimakon sarakunan saudiya suka fara dirar mikayi a kansu.
Mutane da dama sun yi shahada a yayinsa wasu suna gidajen yari a cikin kasar.
342/