1 Nuwamba 2020 - 14:32
Ana Ci Gaba Da Zaman Dar-Dar A Kasar Ivory Coast Bayan Zaɓen Shugaban Kasar Da Aka Gudanar Yau

Rahotanni daga ƙasar Ivory Coast suna nuni da cewa ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasar da ke cike da kace-nace a cikinsa da aka gudanar a yau ɗin nan inda shugaban ƙasar Alassan Ouattara ke neman ta zarce a kan karagar mulkin ƙasar.

ABNA24 : Tun da safiyar yau Asabar ne aka buɗe akwatunan zaɓen a duk faɗin ƙasar don ba da dama da ‘yan ƙasar kaɗa kuri’arsu don zaɓan shugaban ƙasar da zai ci gaba da jagorancin ƙasar.

Shugaban ƙasar Alassan Ouattara, bayan ya kaɗa kuri’arsa ya buƙaci ‘yan ƙasar da su fito su kaɗa na su kuri’un kamar yadda kuma ya kiraye su da su guje wa duk wani abin da zai haifar da tashin hankali a ƙasar.

Shugaba Ouattara dai, wanda yake neman wa’adi na uku na mulkin ƙasar yana fuskantar hamayya ne daga wajen wasu ‘yan takara su uku wato tsohon shugaban ƙasar Henri Konan Bedie da tsohon firayi ministan ƙasar Pascal Affi N’Guessan, waɗanda tun da fari suka kirayi magoya bayansu da su ƙaurace wa zaɓen. Sai kuma ɗan takara na huɗu mai cin gashin kansa Kouadio Konan Bertin.

Rahotanni daga ƙasar Ivory Coast ɗin suna nuni da cewa da dama daga cikin al’ummar ƙasar suna cikin fargabar ɓarkewar rikici a ƙasar kamar yadda ya faru a baya, musamman bayan rahotanni da suke nuni da cewa kimanin mutane 30 ne suka mutu cikin rikice-rikicen da suka faru ‘yan kwanaki kafin wannan zaɓen abin da ya sake tunatar da al’ummar ƙasar rikicin da ya ɓarke bayan zaɓen 2010-2011 da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 3000.

342/