16 Agusta 2016 - 18:40
Kisan kiyashin da sojoji suka yi a Zariya da rawar da gwamnatin tarayya ta taka

Bayan wani taron manema labarai da kwamitin fafutikar ganin an saki Shaikh Zakzaky (H) suka gabatar a Kaduna, inda suka bayyana matsayar Harkar Musulunci a kan rahoto da shawarwarin da Kwamitin binciken jihar Kaduna ya fitar, cikin gaggawa fadar Shugaban kasa ta fitar da nata rahoton, inda ta yi kokarin.

 

Bayan wani taron manema labarai da kwamitin fafutikar ganin an saki Shaikh Zakzaky (H) suka gabatar a Kaduna, inda suka bayyana matsayar Harkar Musulunci a kan rahoto da shawarwarin da Kwamitin binciken jihar Kaduna ya fitar, cikin gaggawa fadar Shugaban kasa ta fitar da nata rahoton, inda ta yi kokarin fitar da kanta daga cikin wadanda ke da hannu cikin kisan kiyashin na Zaria.

Jaridar 'Guardian' ta ranar 12 ga watan Agusta 2016, ta ruwaito cewa mai magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu, "Ya nisanta shugaba Buhari daga tsare Shaikh Zakzaky da aka yi, inda ya nuna cewa hakan al'amari ne na bangaren Shari'a na gwamnatin Jihar Kaduna." Jaridar ta ruwaito Kakakin Shugaban kasar yana cewa, "al'amarin nan bai danganci Shugaban kasa ba, al'amari ne na Jiha kuma Shugaban kasa ba shi da hannu a ciki. Shin ya yi ma'ana a yarda cewa Shugaban kasa ne ya hana a saki Jagoransu bayan cewa, a bisa manufa, Shugaban kasa ya ki yarda ya sa kansa a ciki? Kawai su danganta matsalarsu ga gwamnatin Jihar Kaduna."

Wannan karara ya nuna yunkurin kaucewa daukar alhakin wannan aika-aika, sannan kuma ya kamata shi mai magana da yawun bakin Shugaban kasa ya sake tunani da gaggawa ya kuma je ya binciki gaskiyar abin da ya faru. Tuni dai Kwamitin binciken ya fitar da rahoton Allah wadai a kan kisan kiyashin da sojoji suka aikata. Kodayake kuma ya gaza nuna yatsar tuhuma kan fadar Shugaban kasa yayin da ta bayyana gare su kararar cewa an aikata kisan kiyashin ne bisa umarnin babban Kwamandan askarawan kasar nan kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya bukata. Karyatawar bai yi wa fadar Shugaban kasa kyau ba, domin da a ce da gaske babu sa hannunsa a ciki, kuma fiye da wata tara da suka gabata ya kasa daukar mataki a kan wadanda suka saba dokar kundin mulkin kasa bisa gadara, sannan suka kwace ikon zartarwar sa, wannan hujja ne mai karfi da ya nuna gazawarsa da kuma rashin cikakken ikonsa a kan alamuran kasa.

Kari a kan haka, idan abin a yarda da maganar da Garba Shehu ya fada ne na cewa wannan al'amari ne da ya danganci gwamnatin jihar Kaduna, za mu iya yin daidai idan muka ce Shugaban kasa ya tattara ikonsa na babban Kwamandan askarawan kasar nan ya mika shi ga Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, wanda shi kuma ya jagoranci sojoji a aiwatar da kisan kiyashi na fiye da awanni 48? Shin Garba Shehu na kokarin nuna mana cewa Ogansa ya rasa abin yi ne ko kuma gaza aiwatar da aikinsa kamar yadda ya yi rantsuwa zai zartar? Shin hakan ya kama hankali?

Shugaban kasa, tun bayan kisan bai bar kowa cikin shakku ba a kan sa hannunsa tun daga farko har karshe. Wannan ba wani abu ne da mai magana da yawun sa zai tunanin zai gushe ba. Shugaban kasar tuni ya bayar da kansa. Dole ce ta sanya ya yi magana a kan kisan kiyashin bayan dogon lokaci da ya yi shiru da gangan a kan kisan. Yayin da yake magana da manema labarai, ya kasa boye kiyayya da jin haushin da ke cikin zuciyarsa, wadda ta bayyana karara a fuskarsa. Ya yi kokarin nuna sojoji ke da gaskiya ta hanyar zayyano wasu zargi na shirme, kamar 'kirkirar gwamnati cikin gwamnati' da sauran su. Kuma Shugaban kasar har yanzu bai yi ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe ba, bai kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa ba, duk da cewa kuma binciken 'JCI' ya tabbatar da kisan daruruwan mutane da sojoji suka aikata ba bisa ka'ida ba, wanda kuma shi ne babban Kwamandansu. Bayan ya gama bayyana raayinsa yayin hira da manema labaran, sai ya nemi al'umma da su jira sakamakon Kwamitin binciken, saboda ya san cewa sun gama tsara yadda za su zargi wadanda aka cutar, sannan su wanke maharan.

Sanayyar shugaban kasar kafin faruwar al'amarin ya sake bayyana ne lokacin da ya kai ziyara zuwa kasar Saudiyya, inda aka gan shi tare da mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da kisan ko kuma yabawa kisan a wani abu da ya yi kama da liyafar nasara da jin dadi. Shugaban kasar da kansa ya fada wa tashar talabishin na Al-Arabiyya da ke Qatar cewa gwamnatinsa ta kaddamar da hari a kan 'IMN' ne a watan Disamba saboda sun zama kamar wata gwamnati daban a kasa, kuma suna kara samun kusanci da Iran.

Wani karin hujja da ya tabbatar da cewa Shugaban kasar ba kawai ya san da faruwar abin ba ne, lallai shi ya bayar da umarni, shi ne wani rikidon din magana da aka yi yayin wani zaman sirri a jihar Kebbi, inda wani babban dan Salafiyya ya bayyana wani zaman sirri da suka yi shugaban kasa, inda ya bayyana musu cewa da zarar ya dawo daga Iran zai auka wa ‘yan uwa musulmi na Harkar Musulunci, IMN. Shugaban kasa da mai magana da yawunsa, duk ba su musanta haka ba. Shin haka bai fi kama hankali ba cewa Shugaban kasa na da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin fararen hula da aka aikata a Zariya?

Wani karin tambaya ga mai magana da yawun Shugaban kasar shi ne, me ya sa Hukumar 'DSS' suke tsare da Shaikh Zakzaky da matarsa, idan har babu hannun Shugaban kasa a ciki? Shin 'DSS' yanzu ta zama Hukuma ce a karkashin gwamnatin Jihar Kaduna? Me ya sa sai an nemi izinin Antoni Janar na kasa kafin kowa, har da ma Kwamitin bincike 'JCI' da gwamnatin Kaduna ta kafa kafin a sami damar ganawa da Shaikh Zakzaky, idan har da gaske al'amari ne da ya danganci gwamnatin Kadunan kawai? Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci karkashin jagorancin Sultan din Sakkwato, sai da ta bi ta hannun Sufeto-Janar na 'yan sanda, sannan kuma Antoni Janar da 'DSS' kafin a bar su su gana da Shaikh Zakzaky. Wadannan duk ma'aikatan gwamnatin Tarayya ne ba na gwamnatin jihar Kaduna ba. Ya mai magana da yawun Shugaban kasa zai yi bayanin wannan?

A bayyane yake cewa babban mai magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu, kauce wa gaskiya. Saurin martanin da ya yi a kan wannan muhimmin al'amari akwai wauta cikinsa da kuma yaudara. Ya kamata ne fadar Shugaban kasa ta yi saurin bayyana hakikanin sa hannunta a kisan kiyashin Zaria, ba wai ta hanyar musanta abin da yake a bayyane, sai dai ta hanyar amsar gaskiya da kuma yin adalci ga wadanda abin ya shafa. Fadar Shugaban kasa ta ba da umurnin sakin Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky; da gaggawa ba tare da wani sharadi ba, wanda yanzu haka lafiyarsa na tabarbarewa sosai, tare da duk wadanda ke tsare bisa zalunci a kan wannan al'amari.

Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya
(08050786093)
13/08/2016

Fassarar: Najeeb Umar Maigatari Najeebumar86@gmail.com