Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato ma'aiaktar cikin gidan kasar ta Tunisiya tana sanar da cewa an kashe 'yansandan 4 ne dai a wani harin ta'addancin da aka kai musu a gundumar Tadhawin a kudu masu gabacin kasar.
A gefe daya, majiyar tsaron kasar ta Tunisiya ta sanar a ranar litinin cewa sun yi nasarar hana mutane 1900 'yan asalin kasar ficewa domin shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Kasar Tunisiya dai tana fama da matsalar kungiyoyin 'yan ta'adda.288