4 Mayu 2016 - 14:06
Mutane Da Dama Ne Suka Rasu A Yakin Halab Na Syria

Majiyar labarai daga birnin Halab na kasar Syria sun bayyana cewa yan tabka yaki mai tsanani tsakanin sojojin

Majiyar labarai daga birnin Halab na kasar Syria sun bayyana cewa an tabka yaki mai tsanani tsakanin sojojin gwamnatin Bashar Al-asad da kuma na yan tawaye wanda ya kai ga mutuwar yan tawaye da dama. Majiyar sojojin kasar sun bayyana cewa yan ta'adda sun yi kokarin kwace wani ayanki a cikin birnin Amma sojojin gwamnati suka maida martayi wanda ya kai ga mutuwar yan ta'adda da dama da kuma fararen hula. Labarin ya kara da cewa an dau kusan shekara guda ana  tabka yaki irin wannan tsakanin bangarorin biyu ba.

Wata majiyar yan tawaye ta bayyana cewa sun kashe sojojin gwamnatin syria 40, amma sun kasa rike wani yanki mai suna "Family" a birnin na Halab, bayan sun kwace shi daga hannun sojoji.

Majiyar ta kara da cewa sojojin syrian sun sami dauki daga mayakan Hizbullah kafin su dawo da ikon gwamnatin a cikin garin.288