12 Maris 2016 - 16:53
Bashar Assad ba zai sauka daga kujerar shugabanci Syria ba

Gwamnatin Syria, ta ce makomar shugaban kasar Bashar Assad, ba ya daga cikin abubuwan da za a tattaunawa a taron sulhun da za a fara ranar litinin mai zuwa karkashin inuwar MDD a birnin Geneva.

Ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu’allem, wanda ke gabatar da taron manema labarai a birnin Damascus a wannan asabar, ya ce ba su da niyyar tattaunawa da duk wanda zai diga ayar tambaya a game da makomar kujerar shugabanci ta Bashar Assad.

Rahotanni daga birnin Geneva dai na cewa, ayarin farko na ‘yan adawar wadanda ke da babbar cibiyarsu a birnin Riyad, ya isa a Geneva domin tattaunawar sulhun da za a fara a jibi litinin.288