6 Maris 2016 - 17:18
An Dage Tattaunawar Siriya Zuwa 13 Ga Wata

An dage tattaunawar neman zamen lafiya a Siriya zuwa ranar 13 ga watan nan na Maris.

kamar yadda mai shiga tsakanin a rikicin kasar Mr Stiffan Di Mistura ya sanar a wannan Asabar, ya ce bayan tattaunawa da bangarorin da rikicin ya shafa an dage tattaunawar har zuwa 13 ga wata.

A hannu daya kuma Mr Di-Mustura ya nuna fargabar sa akan yarjejeniyar tsagaita wuta dake tangal-tangal a kasar ta Siriya.

tun da farko dai a ranar 9 ga watan nan ne aka shirya zamen tattaunawar a Geneva tare da halartar wakilan gwamnatin Siriya da kuma na 'yan adawa da zumar samun mafita a rikicin kasar da aka shafe sama da shekara hudu ana yi.288