Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da sama da 500 suka jikkata, kimanin 200 kuma aka zakulo su da rai, a lokacin da ginin mai hawa 17 ya ruguje a garin Tainan.
Mazauna garin sun yi amfani da tsani da kuma wasu kayan aiki a kokarinsu na ceto wadanda ginin ya binne.
Girgizar kasar mai karfin 6.4 ta faru ne da tsakar dare, a yayin da mutane da yawa ke barci.288