Wata kotun daukaka kara a birnin Alkahira na kasar Masar ta warware hukuncin kisa wanda wata karamar kotu ta yankewa shugaban kungiyar Ikhwanul Muslimina wato Muhammad Albadie da wasu mutane 11 a yau Alhamis. Kotun har'ila yau ta warware hukluncin daurin rai da rai da aka yankewa wau mutanen 26, ta kuma bawa mutanen 38 su nemi lauyoyi ko kuma su kare kansu a gaban shari'ar da za'a sake yi masu.
Ana tuhumar mutanen ne da shirya wata makarkashiya ga gwamnatin rikon kwarya wacce sojoji suka kafa bayan kifar da gwamnatin Muhammad Mursi a cikin watan Augusta a zaman nuna rashin amincewa da juyin mulkin da suka yi a masallacin rabi'atul adawiyya na birnin Alkahira.
Jami'an tsaron kasar sun kashe mutane da dama a lokacinda suka yi kokarin tarwatsa taron na masallacin rabi'a.288