13 Janairu 2016 - 04:36
Iran ta kama jiragen ruwan yakin Amurka

Kasar Iran ta kama wasu jiragen yakin Amurka na ruwa biyu dauke da ayarin matuka mutum goma.

Amurka dai ta ce jiragen ruwan na atisayi ne a teku, tsakanin Kuwait da Bahrain sai daya daga ciki ya baci ko lalace, kuma daga nan ruwa ya ja shi zuwa yankin da ke karkashin ikon Iran.

Kuma a cewar Amurka, Sakataren harkokin wajenta, John Kerry na tattaunawa da takwaransa na Iran, wato Mohammad Zarif, kuma ya ba shi tabbacin cewa za a saki matukan jiragen ba da wani bata lokaci ba.

Gidan Talabijin din Iran na harshen Turanci ya ce dakarun juyin-juya-hali ne suka kama jiragen ruwan yakin Amurkan biyu, bayan sun shiga yankin tekun Fasha da ke karkashin ikon Iran, kuma an tafi da su tsibirin Farsi.288