Jiragen yakin Saudiyya suna ci gaba da kai hare-hare akan kasar Yemen. Tashar Telbijin din almasirah ta ‘yan Huthy ta bada labari a jiya laraba cewa; Jiragen yakin Saudiyyar sun kai hare-hare akan yankunan fararen hula da ke gundumar al-Baidhaa a kudancin kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar da dama. A yankin Sa’adah ma dai jiragen yakin na Saudiyyar sun kai hare-haren da su ka dauki rayukan farafen hula masu yawa. A gefe daya sojojin kasar ta Yemen tare da hadin guiwar mayakan Ansarullah sun maida martani akan mayakan da Saudiyyar ta ke goyon baya a gundumar Lahaj tare da kashe 20 daga cikinsu. Watanni 8 kenan a jere da Saudiyyar ta bude yaki da al’ummar Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka masu yawa.288