24 Nuwamba 2015 - 10:31
Turkiyya ta kakkabo jirgin yakin Rasha

Rahotanni na cewa turkiyya ta kakkabo jirgin sojin rasha a kan iyakar kasar syria

Wani kamfanin dillancin labaran Rasha Interfax ya nakalto cewa ma'aikatar tsaron Rasha ta bada sanarwar jirgin yakin samfurin Su-24 ya fadi ne a arewacin Syria, a inda direbobin biyu suka tsira da ran su.

Jami'an rundunar sojin Turkiyya sun ce jirgin saman kasar samfurin F-16s ya harbo jirgin Rasha bayan ya yi masa gargadin kan ya keta sararin samaniyar kasar.

Tun a watan Satumba ne Rasha ta kaddamar da hare-hare ta sama a Syria domin ta taimaka wa Shugaba Bashar al-Assad a yakin da yake yi da 'yan ta'adda. 288