Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin sun jefa hayaki mai sa hawaye a lokacin da suke kokarin shiga cikin masallacin domin kama wadansu Falasdinawa da suka ce suna wurgo duwatsu daga cikin masallacin.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Sojojin sun yi barna a cikin masallacin, to sai dai sun musanta haka tare da fadin cewa kawai sun rufe kofofin masallacin ne domin kulle masu wurge wurgen duwatsun.
Tuni dai hukumomin Isra’ila suka rufe harabar masallacin sakamakon rikicin.289