5 Agusta 2015 - 17:34
Dattawan Borno sun bukaci a tuhumi Jonathan da laifin kisan kiyashi

Dattawan jihar Borno a Tarayyar Najeriya, sun zargi tsohuwar gwmanatin shugaban Goodluck Jonathan da yin ganganci har ‘yan kungiyar Boko Haram suka kashe dimbin jama’a a yankin arewa maso gabashin kasar.Inda suka bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya binciki wannan ba tu sannan kuma a tuhumi masu ruwa da tsaki a harkar tsaron kasar da laifin aikata kisan kiyashi.

Sanarwar da shugaban kungiyar dattawan ambasada Gaji Galtimari ya sanya wa hannu, ta yi ishara da irin kalaman da babban kwamandan askarawan kasar Air Vice Marshall Alex Badeh ya furta da ke cewa sojojin sun fuskanci karancin kayan aiki a lokacin jagorancinsa.

Dattawan sun kuma shawarci Jonathan da ya nemi afuwan Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima, wanda ya sha soka iri-iri da kiraye-kirayen suna marasa dadi kan zargin cewar yana da hannu a ayyukan Boko Haram.

Sun kuma bukaci da a biya al’ummar Borno wadanda ayyukan mayakan ya tagayarasu da iyalansu da wadanda suka rasa rayukansu diya.288