30 Yuli 2015 - 14:20
Hulda Iran da Faransa ta fara Farfadowa

Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabuis ya kai ziyarar aiki a birnin Tehran na kasar Iran, ziyarar da ta tabbatar da kara inganta huldar diplomasiyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Wannan kuma na zuwa ne bayan cim ma yarjejeniyar tarihi kan nukliyr kasar Iran.

Mr Fabuis ya gabatar da wata wasikar gayyata da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya aikawa takwaransa na kasar Iran Hassan Rohani, domin kawo ziyara birnin Paris.

Fabius ya ce Iran da Faransa sun kasance manyan kasashe biyu masu ‘yanci da ke da al’adu mabambanta, gaskiya ne a ‘yan shekarun da suka gabata sakamakon dalilan da kowa ya sani alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, amma yanzu albarkacin yarjejeniyar da aka cim ma ta Nukliya, lamarra za su canza.

Wannan ziyara dai dama ce ta sake farfado da huldodi ta fannoni da dama a tsakanin Faransa da Iran tun daga fanin da ya shafi siyasa da tattalin ariziki daal’adu da kuma Ilimi da huldar diplomsiyar da ke tsakaninsu.288