Kotun da ke zama a garin Gezawa ta bukaci kada a dauki wani mataki kan gwamnan har sai kotun ta saurari bangarorin da ke da ruwa da tsaki a ranar 15 ga watan gobe.
Wasu 'yan Fansho ne a jihar Kano suka shigar da karar tsohon Gwamna Kwankwaso gaban hukumar EFCC suna zargin sa da yin almabazaranci da kudin 'yan fanshon a zamanin da yake gwamna.
A zaman kotun da aka yi da farko a cikin makon nan, lauyan tsohon gwamnan ya shedawa kotun cewa, wanda yake karewa ba ya iya fita daga gidan sa a Abuja saboda tsoron ka da EFCC ta kama shi, abin da lauyan ya ce hakan tamkar tauyewa tsohon gwamnan yancin sa ne.288