Yassin Salhi mai shekaru 35 ya amsa laifin fille kan maigidansa da ya dauke shi aiki tare da rataye kansa a katanga a lokacin da ya kai hari a gabacin Faransa a ranar Juma’ar makon jiya.
Maharin ya ce harin da ya kai baya da nasaba da addini kamar yadda wasu ke kallon harin irin na mayakan da ke da’awar jihadi.
Sai dai kuma mata majiya da ke kusa da masu bincike tace maharin bai yi bayani akan Kabbarar da aka ji ya furta ba a lokacin da ya kai harin na ranar Juma’a a Faransa wanda ya raunana mutane da dama.
Rahotanni sun ce kafin kai harin maharin ya samu sabani da abokin aikinsa, al ‘amarin da ke nuna cewa harin baya da nasaba da tsautsauran ra’ayi. Amma masu bincike sun zanta da mahafiyar Salhi da kanwarsa, wadanda suka ce ya tafi kasar Syria a 2009, kafin barkewar rikici a kasar da kuma bullar mayakan IS.
Yanzu haka dai maharin ya shafe sa’o’i 72 a hannun ‘Yan sanda ba tare da an tuhume shi a kotu ba.288