2 Yuni 2015 - 10:09
jirgin ruwa Chana ya kife a kogi

Wasu Masu aikin ceto a kasar China na kokarin kai taimako kan fasinjojin wani jirgin ruwa 450 wanda ya kife da su a kogin Yangtze bayan karo da guguwa mai karfi. Gidan talabijen na kasar ya sanar da cewar an gano gawawakin mutane 5 yanzu haka, an kuma ceto wasu 10 da ran su.

Ma aikatan ceton sun ce suna samun sakwanni daga cikin jirgin mai hawa bakwai wanda hakan ke nuna cewar mutanen ciki na nan da ran su.ABNA