farko ya kamata ka rika sanya zoben azurfa da dutsen aqiq sannan ka rika sanya shi a hannun dama domin wannan shine Sunnan Annabi {saw}.Wanda ya rubuta littafi mai suna AL- HIDAYA MINAL HANAFIYYA yana cewa:-IN-NAL MASHRU’A AT-TAKATTUMU BIL YAMIN”ma’ana;Abinda aka shar’anta shine sa zobe a hannun dama-LAKIN LAMMAT TAKAZAT HU RAFIDATU JA’ALNAHU FIL YASAR-Amma tunda Rafidawa sun dauki wannan sai muke sanyawa a hannun hagu.Sanya zobe a hannun hagu bada sunan shari’a ba laifi bane amma in kana so ka sanya shi da sunan sunnah sai kuma ka sanya shi a hannun hagu to wannan Bid’ah.Duk wadannan bayanin da muke fadi mun ji sune a harshen Ahlus-sunna wal Jama’a ne. Sannan ance farkon wanda ya fara sanya zobe a hannun hagu domin ya sabama sunna shine Mu’awiya dan Abu Sufyan,wannan yana nan a littafan sunna kuma ba yan shi’a ne suka ce ba.Za mu dakko maku littafan sunna mu karanta maku a cikin wannan bahasin amma ba lallai ya zama a cikin wannan fa’ida ta hudun ba,ku bini bashi. SANYA RAWANI Sannan haka su kayi akan batun sanya rawani.Idan mutum ya sanya Rawani a’ina zai sakko da jelan rawanin?zai sauko shi a gefen dama ne ko zai sauko shi a gefen hagu ne? wane ne Sunna? Al-hafiz Al-Iraqi yace a lokacin da yake bayanin yadda ake sauke rawani cewa “Abinda yake mashru’i a lokacin sauko da rawani shine a sauko da shi ta gefen dama ko ko a sauko da shi ta gefen hagu shine mashru’i?To sai yace;ni a gani na da bincike na (wato Ni Faqihin sunna)Ni ban ga wani dalili ba sam sam wanda yayi nuni akan cewa a sauko da rawani a gefen dama”.A ina ake sauko da gefen rawani kenan?dama ko hagu?. Malaman shi’a in su kayi rawani zaka ga sun sauko dashi ne a gefen hagu basa sauko dashi a gefen dama.To shima wannan malamin sunna din cewa yayi ni banga wani dalili da yayi nuni akan a sanya shi a gefen dama ba sai a wani hadisi mai rauni a wurin Dabarani.Sai shi wannan malamin sunna din yaci gaba yana bayani cewa in ma a kace wannan din ya tabbata,ko kuma mu kace ya inganta to kila shi Annabi{s aaw}yana sauko dashi ne gefen hagu sannan ya yarfa shi zuwa gefen dama din wato ya nada shi kenan a wuyan shi,kamar yadda wasu suke yi.Sai dai sanya gefen rawani zuwa gefen hagu ya zama shi’aar din yan Imamiyyah,sai ya cigaba cewa to tunda ya zama shi’aar dinsu(wato yan shi’a) to ya kamata a guje ma haka din domin kada a yi kama da yan shi’ah. To in kun gane,to daga nan ne suka ce;”Sunnah itace barin yin kama da yan shi’ah wurin yin wannan aikin wato Sunna itace barin sunna”.Me suke nufi?,wato Sunna itace barin sunna-ma’ana Sunnan farkon bata Annabi bace wato ta biyun itace sunna wadda Annabi yayi-wato barin Sunnan Annabi{saa w} itace me? Itace Sunnah a wurin su. Ka gani ko yadda suke kirkiro wata sunna su Sunnatawa mutane binta a matsayin sunna saboda tsawon lokaci kuma ana yin wannan din shi yasa a duk lokacin da wani ya zo da Sunna ta asalin sai ya zama shine ya zo da abinda yake bako. Akwai wasu ababe da suke Sunnan Annabi ne {saw} amma tunda RAFIDA sun karba suna yi sun riqe sai suka bar masu su,sai ya zama cewa suna yin abinda yake ko ba muce akasin wadannan ababen bane amma dai ya sabama wadannan ababen,daga nan ne suka assasa wata Qa’ida wadda take cewa ;-A irin wannan yanayin- da yan shi’a suka riqi wata sunna hart a zama shi’aar dinsu- sabama Sunnah itace Sunnah,wanda wannan yana da ban mamaki da bakuncin gasken gaske.Da yawa daga cikin yan Ahlus-sunna wal jama’a basu san me ake nufi ba da wannan Sunnan ba sannan basu san kuma wace jama’a ake nufi ba da wannan Jama’a din,domin matuqar Sunna ba a jingina ta da Sunnan Manzon Allah{Saaw}ba to ba Sunnan Annabi bace,ta na iya zama Sunnar kowa amma dai ba Sunnan Annabi{saw}bace,Manzon Allah{Saaw} yana cewa:- “MAN SANNA SUNNATAN HASATAN FALAHU AJRUHA WA AJRU MAN AMILA BIHA,MAN SANNA SUNNATAN SAYYI’ATAN FALAHU WIZRUHA WA WIZRU MAN AMILA BIHA”ma’ana “Duk wanda ya sunnata wata sunna kyakkyawa yana da ladan ta da ladan wanda yayi aiki da ita haka yake duk wanda ya sunnata wata sunna mummuna yana wizir dinta da wizir din wanda ya aikata ta,” wato ba tare da an rage wa mai wannan ladan ladan shi da komai ba,wal aksu sahih wato haka wanda ya sunnata mummuna yana da laifin wanda yayi aiki da wannan sunnan mummuna din har zuwa ranar Alqiyama. Kenan Sunna akwai mai kyau da akwai mara kyau,saboda haka in kaji ance Sunna ba dole ya zama Sunnan Manzon Allah{saw}bane kowa yana iya sunnata sunna,wannan daya kenan. Sannan na biyu kuma tana iya zama mai kyau tana iya zama mara kyau kuma Manzon Allah{Saaw} a wani hadisi da Al-imam Muslim ya ruwaito, mai muhimmancin gaske yana ishara zuwa ga wannan haqiqa wadda muke magana a kanta a yanzu,ya zo daga Sahihu Musilim cewa Manzon Allah{saaw} yace:-“LA TATTABI’ANNA SUNANAL-LAZINA MIN QABLIKUM SHIBRAN BI SHIBRIN WA ZIRA’AN BI ZIRA’IN HATTA LAU DAKALU FI HUJIRI GABDIN LAT-TABI’U HUM” ma’ana Manzon Allah{saaw} yana cewa lallai wato ba makawa tabbaci haqiqan zaku dinga bibiyan sunnonin wadanda suka zo gabaninku dantse da dantse, zira’i da zira’i,wato kenan ko ina suka shiga zaku shiga kuma ko me suka yi, irin wannan ku ma za kuyi,ba wata sunna wadda su kayi wadda ba zaku kwafi irinta kuma kuyi ba har ma dai da ace zasu shiga dakin kadangare da za ku bisu ku ma.Kenan wadanda suka zo gabaninku suna da sunnoni ko basu da shi?Tunda suna dashi,wadannan din sunnonin Annabi ne?saboda Annabi {saw} anan wurin yana magana ne akan sunnonin da basu da kyau watoYahudu da nasara wadanda suka zo gabaninku,wato kenan za a canza sunnonin Manzon Allah{saw] da wasu sunnoni.Wannan hadisin yana da gayan kima wurin gane halin da Musulmi suke a yau kuma yana da gayan kima wurin gane Annabcin Manzon Allah{saaw}ta wurin yadda yake bada labarin Mustaqbal.Ala kulli hal ba akan hadisin nake so inyi magana ba,ina magana ne akan SUNAN,lafazin SUNAN da yazo a hadisin “LA TAT-TABI ANNA SUNAL LAZINA MIN QABLIKUM,” a nan wurin ne muke so mu ce ba wai kowace Sunnace take Sunan Annabi{saaw} ba matuqar ba ta jinginu zuwa ga Annabi{saw] din ba to ba Sunnar shi bace. In aka ce Sunna itace sabama Sunna,to ai Sunnar farkon ba Sunna bace,ala kulli hal dai ba Sunnar Manzon Allah{SAW}bane saboda in ka lura anan mun ambaci Sunna guda biyu ko?shine cewa Sunna itace sabama Sunna,in ka lura wadda aka sabama wa itace ta Annabi {saw} ai,wannan ta biyu itace ta Annabi,ta farkon ba ta Annabi bace.Bari in baku misali ;-Imam Fakrur-razi Ash-shafi’i a bangaren fiqhu amma Al-ash’ariy a Aqidah ba dan shi’ah bane,yana cewa a cikin tafsir din shi mai suna At- tafsirul Kabir“ANNA ALIYA BN ABI DALIBIN RA KANA YAJHARU BIL BASMALATY WA QAD SABITA BIT- TAWATIR”ma’ana cewa Imam Ali{as} yana bayyana basmala a cikin sallolin da ba a bayyana karatu a cikinsu wato salloli Ikfatiyya,to Farkru-razy yace wannan ya tabbata da tawatur wato mutawatiri ne kowa ya san haka Ali {as} yake yi,sai ya cigaba Imam Fakru-razy yana cewa “WA MAN IQTADA FI DINIHI BI ALIYI BN ABI DALIBIN RADIYALLAH ANHU FI DINIHI FA QAD IHTADAH” ma’ana Kuma duk wanda yayi koyi da Aliyu bn Abi Dalibi a addinin shi to hakika ya shiriya. Dalilin na,in ji Al-imam Fakarur-razy;shine fadin Manzon Allah{SAW} cewa. ALLAHUMMA ADIRUL HAQQA MA’A ALIYUN HAISU MA DAR ma’ana Ya Allah jujjuya gaskiya da Ali duk inda ya juya,ba jujjuya Ali da gaskiya ba fa- jujjuya gaskiya inda ali yake-wannan ba mu muka fadi ba fa.Al-imam Al-fakrur-razy, ya fadi,shima cewa yayi haka Manzon Allah{SAW}ya fadi.To tunda haka ne,kenan gaskiya tana barin Ali?gaskiya ba ta barin Ali.Al-imam Fakrur-razy yace wannan shine dalili na kuma yace in kayi haka ka shiriya. To don Allah yau ana yi?ana ijhar da basmala a salloli ikfatiyya ma’ana ana bayyana basmala din?to shi kuma Imam Ali daga ina ya samo?daga gaskiya ko daga badil? Saboda haka an cancanja sunnonin Manzon Allah {SAW}.Bari ka ji wani daga cikin zantuka kafin inje inda nake so inje.Abin da nake so inje a wannan fa’idan fa nake nufi ba wai a asalin bahasin mu ba.Yana cewa tabbas gaskiya ne akan cewa dukkan sunnonin Manzon Allah{saw} gabaki dayan su an cancanja su har da sallah shi yasa dan shi’a ya zama maka baqo ba wai don dan shi’a baiyin addini bane.In muna so mu kafa hujja da wannan zamu iya kafawa da Imam Ash- shafi’i ba ma Al-imam Fakrur-razy kawai ba. Imam Shafi’i da kan shi ya ruwaito a littafin shi mai suna AL-UMM ta hanyar Wahab Ibn Kisan yana cewa:-“Ni naga Ibn Zubair yana fara sallah kafin yayi huduba,sannan ya cigaba da cewa KULLU SUNAN MIN SUNANIR RASULIL-LAH QAD GUYYIRAT,HAT- TAS SALAH ma’ana duk sunnonin manzon Allah {saw] gabaki dayan su an canza su har sallah.”Zan dawo zuwa ga wannan in kara maku bayanai akan haka wannan saboda ku gane cewa ba dole bane abinda kaga ana yi a yanzu ya zama cewa shine abin da Manzon Allah{SAW} yayi,kuma ba dole bane ya zama shine abinda Abubakar As-siddiq ya kasance yana yi,ba dole bane ya zama abinda Umar dan Kaddab ya kasance yana yi ba,ba dole bane ya zama abinda Usman dan Affan ya kasance yana yi. Haqiqa ce wannan.Saboda irin wannan ne yasa kaga yan shi’ah sun zama maka baqi,ba wai don saboda su kafirai bane. ABNA
...........
288