Mayakan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari gidan iyalan Abutir da ke yankin Al-Sanati da ke gabashin Khan Younis.
Muhammad Hadi al-Masri dan kasar Falasdinu ya yi shahada a wani harin da aka kai ta sama a mashigar Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza.
Hakazalika sojojin mamaya sun kai hari a wani gida da ke kusa da asibitin gwamnatin Jenin tare da kama mutane da dama.
Harin da sojojin mamaya suka kai a sansanin Nuseirat ya yi sanadiyar shahadar Bafalasdine guda tare da jikkata wasu da dama, wadanda aka kai su asibitin Al-Awda.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta harba manyan bindigu a yankin gabashin Deir al-Balah, kuma wani Bafalasdine ya yi shahada a wani harin da jirgin sama ya kai a yankin Abbasan al-Kabeera da ke gabashin birnin Khan Yunus.
Sannan jiragen saman gwamnatin mamaya sun kai hari a yankin da ke kusa da masallacin Osama al-Najjar da ke Qayzan a kudancin Khan Yunis sau biyu.
Asibitin Al-Awda da ke sansanin Nussirat ya sanar da shahadar wani yaro yayin wani hari da makamin roka da Isra'ila ta kai kan wasu 'yan kasar a yankin Al-Zahra da ke arewacin sansanin.
A yankin Al-Zawaida da ke tsakiyar zirin Gaza an kai harin ne da jiragen sama marasa matuka, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Palasdinawa hudu tare da jikkata wasu da dama.
Dakarun mamaya sun kai hari a yankunan arewacin birnin Gaza, kuma a lokacin da aka kai hare-hare ta sama a yankin Al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza, Falasdinawa biyu sun yi shahada tare da jikkata wasu da dama.
Your Comment