Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Al'ummar kasar Yemen a jiya juma'a sun sake gudanar da jerin gwano a fadin kasar, inda suke jaddada goyon bayansu ga Falasdinawan tare da yin Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kaiwa kasarsu.
Dubban jama'a a birnin Sana'a sun cika babban dandalin birnin a ranar Juma'a a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare ta sama kan kasar ta Yamen.
Suna ɗauke da tutocin Yemen da na Falasdinu tare da rera taken yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Al'ummar kasar Yemen dai sun ce za su ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan Falasdinu duk da hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasarsu, inda suka jaddada cewa harin ya kara karfafa goyon bayansu ne kawai ga Falasdinu.
Akram al-Dhabibi mutumin Yemen mai fafutuka ya ce "Duk da hare-haren da Amurka ke kai wa kasarmu, mun fito daga karkashin harin bamabamai, daga karkashin baraguzan gine-gine, da kuma raunukan da ke zubar da jini".
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen, inda suka bayyana aniyarsu na daukar fansa da dakarun kasar Yemen din suka kai kan yankunan da aka mamaye da kuma jiragen ruwan Isra'ila da jiragen yakin Amurka.
‘Yan kasar Yemen dai na gudanar da tarukan goyon bayan Falasdinu kusan kowace Juma’a tun farkon yakin kisan kare dangi a Gaza a watan Oktoban 2023.
Your Comment