Ruwaya Daga Muhammad Dan Arafah Yace Naji Abal Hasan Imam Ridha As Yana Cewa: Manzon Allah {Sawa} Ya Kasance Yana Cewa: “ Idan Al’ummata Suka Ki Yin Umarni Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummuna Aiki ( Wannan Yace Ai Wancen Bai Yiba Nima Bazan Yiba Har Yazamo Ba Wanda Yayi) To Su Saurari Saukowar Azaba Daga Wajen Allah” Attahzib, Juzi Na 6 Shafi Na 177.
Wace Irin Azaba Kenan Shin Kamar Dutse Ne Da Zai Sauko Daga Sama Ko Kuwa? Ah Ah
Azabar Allah An Fassara Ta A Cikin Alkur’ani Inda Allah Ta’ala Yake Cewa:
قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَىٰ أَنْ يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَابًا مِنْ فَوْقِكُمْ أَوْ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعًا وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْضٍ ۗ انْظُرْ كَيْفَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ لَعَلَّهُمْ يَفْقَهُونَ سورة الأنعام، الأية : 65.
Ka Fada Masu Allah Mai Iko Ne Kan Ya Aiko Maku Da Azaba Daga Samanku ( Wato Daga Sama) Ko Daga Karkashin Kafafunku ( Wato Ta Kasa) Ko Kuma Ya Sanya Maku Rigar Rarraba Ya Dora Wasu A Kanku Ko Kuma Ya Dandanawa Sashen Junanku Azaba Da Wani Sashen…
Idan Muka Duba Ma’anar Wannan Ayar Cikin Ruwayoyi Zamu Ga Abinda Take Nufi Shine:
Azabar Da Zata Zo Daga Itace Salladuwar Wadanda Suke Samanku Shugabanni Akanku
Azabar Da Zata Zo Kuma Daga Kasa Itace Salladuwar Sauran Mutane Wadanda Ba Shugabanni Ba.
Yanzu Fa Abunda Muke Ciki Kenan Ga Azabtarwa Shugabanni Ga Kuma Ta Talakawa Yan Kuci Kubamu
Daga Littafin Ustaz Shaheed Mudahhari Rh, Hamaseh Husainy Juzi Na 1, Shafi Na 201.
Allah Yasa Mu Anfana Mu Gyara Halayenmu Da Yin Umarni Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummunan Sa.
Imam Bakir As Yana Cewa:
A Karshen Zamani Zai Kasance Za'ai Wasu Mutane Da Za'ana Binsu Yi Masu Biyayya (A Matsayinsu Na Malamai Ko Shugabanni) Wanda Zaka Samesu Suna Kokari Wajen Karatun Alkul'ani Da Yin Ibadah Sosai Amma Don Riya Sukeyin Hakan, Sunzo Daga Baya Sune Cukakkun Wawaye.
Basa Wajabta Yin Umarni Da Kyakkyawan Aiki Basa Hani Da Mummunan Aiki Sai Dai Idan Sun Ga Zasu Shiga Matsala ( Abun Zai Shafesu Kana) Suke Yin Hakan Suna Nemawa Kansu Samun Sauki Da Uzurirrika Zaka Ganzu Suna Maida Hankali Kan Yin Sallah Da Azumi Da Duk Abin Da Ba Zai Cutar Da Jikinsu Ba Ko Dukiyarsu Suna Bin Kuskuren Malamai Da Gurbatar Aikinsu, Da Sun San Sallar Ma Da Ibadun Da Suke Yi Zai Cutar Dasu A Jikinsu Da Dukiyarsu Da Sun Bar Shi Ba Su Yi Ba, Kamar Yadda Suka Bar Mafi Girma Da Daukakar Faraloli ( Wato Umarni Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummuna) Domin Shi Umarni Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummuna Farillah Mai Girma Ce Domin Da Aikata Tane Sauran Farillai Suke Tsayuwa Kuma Ta Wannan Ne Hanyoyi Suke Samun Aminci Kuma Arzuka Su Yalwata Kuma Korafe-Korafen Mutane Su Karanta Kasa Ta Rayu Ayi Adalci Ga Al’umma, Lamari Ya Daidaita. Rashin Aiki Da Wannan Ta Nan Fushin Ubangiji Yake Cika Da Tabbatuwa Akan Al'ummah, Sai Ukubarsa Ta Hade Kowa Da Kowa Ya Zamo Wanda Suke Kubutatttu Sun Halaka A Cikin Fajirai Da Yara A Cikin Manya Domin Shi Horo Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummunan Aikin Tafarki Ne Na Annabawa Da Salihan Bayi Don Haka Ku Ki Mummunan Aiki Da Zukatanku Ku Furata Hakan Da Harsunanku Ku Tsananta A Garesu Kwarai Akan Hakan Kada Kuji Tsoron Zargin Mai Zargi Cikin Umarnin Ubangiji Idan Sun Wa'aztu To Sun Koma Zuwa Ga Gaskiya Ba Ku Da Hanya Akansu Sai Ku Kyalesu. Domin Allah Ta'ala Yana Cewa:
إنما السبيل على الذين يظلمون الناس ويبغون في الأرض بغير الحق أولئك لهم عذاب أليم
Idan Kuma Suka Ki Yin Hakan To Sai Ku Shiryar Da Su Da Jikkunan Ku, Ku Kisu Da Zukatanku, Ba Tare Da Kuna Nufin Samun Mulki Ko Kuma Neman Dukiya Ba Bakuma Yin Zalunce Ta Hanyar Samun Nasara Akansu Ba Da Yin Zalunci Da Yin Hakan Ba, Sai Dai Yin Adalci Har Sai Sun Dawo Zuwa Ga Al'amarin Da Allah Ya Umarcesu Da Shi Suna Masu Biyayya Gare Shi.
Allah Taala Ya Tabbatar Damu Bisa Umarni Da Kyakkyawan Aiki Da Hani Da Mummunan Aiki Ya Kare Mu Daga Zamewa Daga Kan Tafarkinsa
Your Comment