Kamfanin yada labarai na harshen Ibrananci Yedioth Ahronoth ya ba da rahoton shigar da tuhume-tuhume da dama a cikin nau'i na laifukan leƙen asiri guda 35 don goyon bayan Iran; shari'o'in da suka fara bayyana a bainar jama'a tun daga watan Satumba na 2024.
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar rahoton, wasu 'yan ƙasar Isra'ila, ciki har da waɗanda ke aikin tsaro da sojoji da kuma waɗanda aka ajiye na rundunar sojojin Isra'ila sun bai wa Iran bayanai masu mahimmanci da takardu da suka shafi ma'aikatu da cibiyoyi. An kuma aika wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma don gudanar da ayyukan tsaro har ma da ayyukan kisan kai, wanda a ƙarshe bai faru ba.
Your Comment