Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Sama da birane 80 na kasar Spain ne aka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga samar da zaman lafiya na dindindin a Falasdinu da kuma yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a zirin Gaza.
Dubban 'yan kasar Spain ne suka hallara a manyan wuraren manyan biranen kasar Spain, musamman a birnin Madrid, babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu.
Mahalarta zanga-zangar sun yi kira ga duniya baki daya da su dakatar da kisan gillar da ake yi wa al'ummar Palasdinu. Sun kuma rike tutocin Falasdinu da allunan da aka rubuta "Netanyahu Mai Laifi. Ta'addanci" "Dole ne a 'yantar da Falasdinu," da "zaman lafiya".
Your Comment