Girgizar kasa mai karfin awo 7.7 ta afku a Myanmar da wasu sassa na kasar Thailand a jiya Juma'a a kalla mutane 1,000 ne suka mutu yayin da wasu daruruwa suka jikkata.
Girgizar kasa mai karfin awo 7.7 a Myanmar bisa binciken farko na yanayin kasa na Amurka: Kimanin mutane 800,000 a Myanmar, China, da Thailand suka ji girgizar kasa mai karfin 7.7.
An kiyasta cewa dubban mutane ne suka mutu a girgizar kasar. Har yanzu dai ba a bayyana wani rahoto a hukumance kan yawan barna da asarar rayuka a wadannan kasashe uku ba.
Girgizar kasar da aka kuma ji a Bangkok, babban birnin kasar Thailand, a makwabciyar kasar Myanmar, mai tazarar kilomita fiye da 1,000, ta kashe mutane akalla 9.
Kasar Burma wanda yanzu aka santa da Myanmar kasa ce da ke kudu maso gabashin Asiya mai kabilu sama da 100, tana iyaka da Indiya, Bangladesh, China, Laos da Thailand. Yangon shi ne birni mafi girma a ƙasar, ƙasar kasuwanci mai cike da jama'a, wuraren shakatawa da tafkuna masu yawa, da kuma babban dutsen Shwedagon Pagoda, wanda ya ƙunshi kayan tarihi na Buddha da tarihinsa ya ke danganawa da karni na 6.
Your Comment