1 Satumba 2025 - 21:21
Source: ABNA24
Yemen: Mun Kai Wa Wani Jirgin Ruwan Isra'ila Hari

Rundunar sojin Yaman ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin ruwanta sun kai hari kan jirgin ruwan dakon mai na Isra'ila Scarlet Ray a arewacin tekun Bahar Maliya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar sojin Yaman ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa sun kai farmaki kan jirgin ruwan dakon mai na Isra’ila mai suna Scarlet Ray a arewacin tekun Bahar Maliya.

Rundunar sojin Yaman ta kara da cewa: An kai harin ne da makami mai linzami da ya kai kan jirgin Isra'ila kai tsaye da ikon ga Allah.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Za mu ci gaba da tallafa wa al'ummar Palasdinu ta hanyar hana shige da ficen jiragen ruwan Isra’ila ko jiragen ruwan da suke nufar tashar jiragen ruwa na Falasdinawa da ke mamaye da su. Za mu ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da Isra'ila ta mamaye a Falasdinu.

Wani bangare na sanarwar kuma ya kara da cewa: Za a ci gaba da gudanar da ayyukanmu har sai an daina wuce gona da iri da kuma kawar da duk wani shingen da aka yi wa al'ummar Palasdinu a zirin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha