10 Maris 2025 - 10:06
Source: ABNA24
Isra’la Na Ci Gaba Da Gina Sansanonin Soji A Labnon

Cikakkun bayanai na sabuwar mamayar da Isra'ila ta yi wa Lebanon; Tun daga gina wuraren soja zuwa killlace wasu yankunan.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare da wuce gona da iri kan yankin Lebanon ta hanyoyi daban-daban, kuma ta hanyar gina wuraren soji, da hakar magudanar ruwa da ramuka, da kuma samar da wuraren da tsaro, suna masu yunkurin zana sabon layin "Blue Line" (layin Majalisar Dinkin Duniya da aka shata kan iyakar Lebanon da yankunan da aka mamaye).

Jaridar Al-Akhbar ta kasar Labanon a yau Litinin ta rubuta a cikin rahotonta game da halin da Isra'ila ke ciki a kudancin kasar Lebanon da kuma take hakkin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar cewa: Ta'addanci da keta hurumin Isra'ila ya hada da kai hare-hare ta sama da na bindigogi da harbe-harbe kan fararen hula na kasar Lebanon da ke tunkarar matsugunan Isra'ila ko yankunan da Isra’ala ta kafa a kasar Lebanon. Ci gaba da tona magudanan ruwa da ramuka, da samar da katangar soji, da suka hada da shimfida nakiyoyi da kafa igiya, wasu misalai ne na kutsawa yankunan kasar Labanon da gwamnatin sahyoniya ta yi.

A wani gagarumin ci gaba na baya-bayan nan, makiya yahudawan sahyoniya sun tona ramuka da magudanan ruwa a yankin Dasht al-Khayyam da yankin Sarda da ke yammacin kasar Lebanon. Wasu daga cikin wadannan magudanan ruwa na da nisan kilomita daya daga katangar kan iyaka, yayin da wasu kuma ke da nisan mil dari, kuma tsawonsu ya kai kimanin kilomita bakwai.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha