8 Maris 2025 - 04:53
Source: ABNA24
Turai: Bai Kamata Hamas Ta Mulki Gaza Ba, Ko Ta Zama Barazana Ga Isra'ila Ba.

Ministocin harkokin wajen kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka yi maraba da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza tare da bayyana shi a matsayin batun gaskiya.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, sanarwar da aka buga a shafin yanar gizon ma'aikatar harkokin wajen Jamus a ranar Asabar din da ta gabata ta bayyana cewa: "Mu ministocin harkokin wajen Faransa, Jamus, Italiya da Birtaniya muna maraba da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na gabatar da wani shiri na sake ginawa da farfado da yankin Gaza". "Wannan shiri ya ayyana sahihiyar hanya don sake gina Gaza, kuma idan aka aiwatar da shi, zai yi inganta samun ci gaba cikin sauri kuma mai dorewa a cikin mawuyacin halin rayuwa na Palasdinawa da ke zaune a yankin".

Sanarwar ta ci gaba da jaddada cewa: “Dole ne a yi kokarin farfado da aikin sake gina kasa bisa ingantaccen tsarin siyasa da tsaro wanda bangarorin biyu suka amince da su; "Tsarin da ke ba da tabbacin zaman lafiya da tsaro na dogon lokaci ga bangarorin biyu".

A yayin da suke nanata matsayinsu na kiyayya ga kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu, kasashen Turai hudu sun bayyana cewa: Muna da matsaya kai tsaye cewa bai kamata Hamas ta mulki Gaza ba, kuma kada ta zama barazana ga Isra'ila. "Muna goyon bayan babbar rawar da hukumar Palasdinawa ta taka da aiwatar da ajandar sake fasalinta".

Sanarwar ta kuma kara da cewa: "Muna matukar godiya da kokarin da dukkanin bangarorin da abin ya shafa suka yi, muna kuma godiya ga muhimmin sakon da kasashen Larabawa suka aike ta hanyar tsara wannan shiri tare." Mun himmatu wajen yin aiki tare da wannan shiri na Larabawa, Falasdinawa, da Isra'ila don magance batutuwa daban-daban, ciki har da tsaro da shugabanci. "Muna kira ga dukkan bangarorin da su dauki wannan shiri a matsayin mafari don ci gaba da kokari".

Shirin sake gina Gaza, wanda kasashen Larabawa suka gabatar, wani cikakken shiri ne na dalar Amurka biliyan 53, na sake gina zirin Gaza nan da shekara ta 2030. Shirin wanda aka amince da shi a taron kungiyar kasashen Larabawa a birnin Alkahira, ya hada da share tarkace, kwance bama-bamai da ba a fasa su ba, gina gidaje masu dorewa, da bunkasa yankunan masana'antu, tashar jiragen ruwa, da filin jirgin sama.

Babban makasudin wannan shiri dai shi ne sake gina Gaza ba tare da raba mazaunanta da matsugunansu ba da kuma inganta rayuwar Palasdinawa a yankin. Shirin dai na zuwa ne bayan da a baya shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wata shawara mai cin karo da juna, inda ya bukaci a kwashe mazauna Gaza tare da mayar da yankin wurin yawon bude ido a gabar teku.

Your Comment

You are replying to: .
captcha