Ministan harkokin wajen Oman Badr Al-Busaidy ya sanar da cewa: Muna adawa da shirin korar al'ummar Palastinu daga zirin Gaza.
Jassim Mohammad Badiwi, babban sakataren kungiyar hadin kan yankin tekun Fasha ya bayyana cewa; Ba zai yiwu a kori da shafe Falasdinu daga taswirar ba, kuma muna kira da a aiwatar da shirin zaman lafiya na Larabawa.
Shima Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya yi bayanin cewa: Dole ne shirin korar Falasdinawan ya fuskanci tsattsauran adawar Larabawa domin manufarsu ita ce ta lalata hakkokin Falasdinawa da kuma batun Falasdinu.
Irin wadannan tsare-tsare dai sun ci karo da dokokin kasa da kasa, kuma babu wanda zai iya korar al'ummar Palasdinu daga kasarsu.
Muna ayyana adawarmu mai ƙarfi ga duk waɗannan tsare-tsare kuma za mu tsaya tsayin daka tare da Masar, Jordan, da Saudiyya.
Har ila yau, Ahmed Aboul Gheit, babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa ya jaddada cewa: Makasudin taron shugabannin kasashen Larabawa da aka gudanar a yau shi ne jaddada adawa da shirin korar Falasdinawan da kuma gabatar da wasu hanyoyi daban-daban, kuma shirin Larabawa da aka gabatar a wannan taro na da damar daidaita al'amuran da ke faruwa.
Dangane da wannan batu shi ma ministan harkokin wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya bayyana cewa: Muna matukar adawa da shirin korar Falasdinawa daga kasarsu, muna kuma jaddada cewa kokarin raba Gaza da kasar Falasdinu ba shi da amfani kuma ba za a iya aiwatar da hakan ba.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya ce: Muna adawa da take hakkin al'ummar Palasdinu, kuma babu wani bambanci wajen aiwatar da hakan ta hanyar gina matsuguni ne, ko mamaye filaye, ko yunkurin korar Palasdinawa.
Muna jaddada bukatar samun garantin kasa da kasa don ci gaba da tsagaita bude wuta a Gaza da kuma hana sake barkewar yaki a yankin.
Shi ma yarima mai jiran gado na Kuwait Sabah Khalid Al-Sabah ya jaddada a kan haka: Dole ne komitin sulhu ya dauki matakin dakatar da hare-haren da Isra'ila ke kai wa zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.
Dole ne mu dauki matsaya daya tak a matsayin ƙasashen larabawa domin tinkarar shirin korar Falasdinawa da ruguza batun Palasdinu.
Har ila yau, dole ne mu gabatar da wani shiri na sake gina zirin Gaza wanda ya hada da dukkan bangarorin Rayuwar dan Adam da tattalin arziki.
Muna kuma jaddada bukatar hadin kan cikin gida a Falasdinu, gami da yarjejeniya kan yadda za a gudanar da mulkin zirin Gaza.
Bayan gudanar da wannan taro Gwamnatin Sahayoniya ta nuna adawarta ga shirin kasashen Larabawa dangane da Gaza
Bayan kammala babban taron na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Alkahira da inda dukkanin ƙasashen suka amince da shirin kasar Masar na sake gina Gaza, ma'aikatar harkokin wajen kasar Isra'ila ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana adawarta da shirin kasashen Larabawa na tafiyar da al'amura a Gaza.
Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta yi ikirarin cewa sanarwar karshe na taron kungiyar kasashen Larabawa ba ta yi la'akari da hakikanin abin da ke faruwa a Gaza ba, kuma Hamas ba za ta iya ci gaba da zama a Gaza ba.
Ma'aikatar ta kuma yi nuni da cewa sanarwar taron na birnin Alkahira ba ta ambaci harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba ba, tana mai cewa an shirya wannan bayani ne bisa matsayin hukumar Palasdinawa da hukumar UNRWA.
Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta yi kira da a karfafawa al'ummar Gaza gwiwa kan amincewa da shirin shugaban Amurka Donald Trump na yi masu hijirar dole daga kasarsu.
Your Comment