5 Maris 2025 - 13:42
Source: ABNA24
Shugabannin Kasashen Siriya Da Lebnon Sun Tattauna Kan Yadda Zasu Sarrafa Iyakoki Tsakanin Lebanon Da Siriya

Shugabannin kasashen Lebanon da Syria sun tattauna batun kula da iyakokin kasashensu a wata ganawa.

A cewar ISNA, a gefen taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa a birnin Alkahira kan batun zirin Gaza, shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya jaddada wajabcin kula da iyakokin bai daya a ganawarsa ta farko da Ahmed al-Sharaa, wanda aka fi sani da Abu Muhammad al-Julani, shugaban kungiyar Tahrir al-Sham kuma shugaban rikon kwarya na kasar Syria.

Kasashen Lebanon da Syria dai na da iyaka da ke da tsawon kilomita 330, galibi musamman a arewa maso gabashin Syria, ba suda iyaka, wanda hakan ya sa masu fasa-kwauri, da mafarauta, da ma ‘yan gudun hijira ke shiga cikin sauki.

Ofishin shugaban kasar Lebanon ya sanar a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin sada zumunta na X cewa, shugabannin kasashen Lebanon da Syria sun tattauna wasu batutuwan da ba a warware su ba a yayin ganawar.

Sanarwar ta ce, a yayin ganawar, an cimma matsaya kan daidaitawa tsakanin kasashen biyu ta hanyar kwamitocin hadin gwiwa da za a kafa bayan kafa sabuwar gwamnatin Syria, kuma bangarorin biyu sun jaddada wajibcin kula da iyakokin kasashen biyu da nufin dakile duk wani nau'in wuce gona da iri.

Sabbin hukumomin kasar Syria wadanda ke cikin bangaren 'yan adawa masu dauke da makamai kuma suka karbe iko da kasar bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria a watan Disambar 2024, sun sanar a watan Fabrairun fara aikin tsaro a yankin kan iyakar Homs da nufin rufe hanyoyin safarar makamai da kayayyaki.

Your Comment

You are replying to: .
captcha