5 Maris 2025 - 10:13
Yakin Cikin Gida A Isra’ila Tsakanin Yan Majalissa Da Natenyaho Yana Kara Kamari

Hukumar tsaro ta Shin Bet ta fitar da takaitaccen binciken da ta gudanar kan gazawar jami'an tsaron Isra'ila a harin da aka kai ranar 7 ga watan Oktoba.

Yair Lapid, Jagoran 'Yan Adawar Yahudawan Sahyoniya Ya Ce Wa Netanyahu: "Ba A Ba Ku Damar Tsayawa A Nan Ku Yi Wa Kowa Ihu Irin Wannan Ba!"

Ya kara da cewa: "Mai girma Minista, ka shawarce ni ba da dadewa ba da cewa kada in sarrafa fushi na a bayyanar jama’a, wasan kwaikwayon da na gani yayi min wuyar gani kuma ban ji dadin ganinsa ba. Ka dan dakata!".

Netanyahu ya mayarda martini da cewa: Kuna tsammanin mu yara ne, kwamitin gwamnati da ke binciken ranar 7 ga Oktoba ba shi da wata hanya ta nuna son kai.

Netanyahu ya fusata matuka dangane da kalaman da wasu mambobin Knesset suka yi game da kwamitin gwamnati da ke binciken abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, yana mai cewa:

"Kuna ganin mu yara ne? Kuna ganin wannan kwamiti ne na gwamnati? Mu muna bukatar kasa ta hakika ne al’umma suna neman gaskiya ne, muna son kwamitin da zai binciki komai kuma ya yi shi ba tare da nuna son kai ba".

 Kwamandan sashin ayyuka na sojojin Isra'ila ya yi murabus saboda shan kayen da Isra’ila ta sha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Majiyoyin yaren yahudanci sun sanar da cewa, Odid Besiuk, kwamandan sashin ayyuka na sojojin Isra'ila, ya mika takardar murabus dinsa bayan babbar nasarar da Hamas ta samu a harin na ranar 7 ga watan Oktoba. Wadannan majiyoyin sun jaddada cewa shugaban hafsan sojin ya amince da murabus din.

Manazarta suna ganin hakan da cewa: Sakamako na bincike na 7 ga Oktoba ya nuna ƙwarewar Gwagwarmaya ne sosai.

Rashin yin hasashen harin, da shirye-shiryen tunkararsa, da yadda za a tunkari shi kafin faruwar lamarin, shi ne binciken da sojojin mamaya suka yi kan harin na ranar 7 ga Oktoba; Harin da dakarun Qassam suka kai wanda ya kai ga fadowar yankunan da ke makwabtaka da Gaza cikin 'yan sa'o'i.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Ibraniyawa na cewa, binciken da sojojin mamaya suka yi kan dalilan da suka haddasa wannan shan kashi ya hada da nazarce-nazarce guda 77, wanda aka kasa su zuwa rukuni hudu: binciken gama-gari da na leken asiri, da tsarin yanke shawara a daren da aka kai harin, da kuma yadda sojojin suka gudanar da ayyukansu.

Wannan bincike ya nuna babbar gazawar soji a dukkan matakan tsaro, soji, da leken asiri, ba tare da sojojin mamayan sun iya tunkude ko hasashen wannan harin ba; Batun da a karshe ya haifar da faduwar yankunan da ke daura da Gaza cikin kankanin lokaci.

Wani mai sharhi kan harkokin soji da dabaru Yousef Al-Sharqawi a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Safa ya ce: Binciken da sojojin Isra'ila suka yi a ranar 7 ga watan Oktoba ba su bayar da cikakkiyar labarin abunda ya faru ba, musamman ganin cewa an fitar da rahotannin da ke nuni da cewa wani hadadden shan kasha ne ya faru ta sama da kasa da kuma teku ya yi tasiri a kan aikin sojojin mamaya.

Al-Sharqawi ya kara da cewa: Nazari 77 da sojojin mamaya suka gudanar sun yi nazari kan yadda za a iya kai hari kan Isra'ila ba tare da jami'an leken asiri sun yi hasashen hakan ba.

Ya ci gaba da cewa: Hamas sun yi galaba a harin ba-zata na ranar 7 ga watan Oktoba domin kuwa jami’an leken asiri na sojin Isra’ila da dukkan sassan tsaron kasar sun kasa yin hasashen wannan harin. Gwagwarmaya ta tunkari inda aka kai musu hari ta hanyar kai hare-hare cikin sanda, a lokacin da ya dace, ta katse sandan na ta tare da kaddamar da manyan hare-haren ta.

A daya hannun kuma, mai sharhi kan harkokin siyasa Amjad Bashkar ya ce: gazawar da Isra'ila ta yi na leken asiri a ranar 7 ga watan Oktoba, wani babban kaduwa ne ga gwamnatin kasar da jami'an tsaronta, musamman ganin cewa Tel Aviv ta dogara kacokam kan bayanan sirri da fasaha wajen sanya ido a Gaza, to sai dai lamarin ya nuna gazawa sosai a tsarin tsaron Isra'ila tare da nuna fifikon gwagwarmayar Palasdinawa a cikin tsare-tsare da aiwatar da ayyukanta.

Bashkar ya danganta wannan gazawar, bisa yadda Isra'ila ta amince da ita, da dogaro da fasahar kere-kere, yana mai cewa: "Isra'ila, wacce ta dogara kan sa ido da fasahohin leken asiri, ta kasa yin amfani da sinadarin dan Adam, kuma hakan ya ba da dama ga gwagwarmaya wajen aiwatar da tsare-tsarenta gaba daya da kuma bayanan sirri".

Shin Bet ta fitar da sakamakon bincikenta game da shan kayen 7 ga Oktoba

Hukumar tsaro ta Shin Bet ta fitar da takaitaccen binciken da ta gudanar kan gazawar jami'an tsaron Isra'ila a harin da aka kai ranar 7 ga watan Oktoba.

A cewar jaridar Times of Israel, Shin Bet ta yanke shawarar cewa akwai gazawa a cikin ma’aikatar tsaro, amma yawancin gazawar na wasu hukumomin gwamnatin Isra'ila ne.

Daga cikin dalilan da rahoton ya kawo na kasawar ranar 7 ga watan Oktoba akwai:

Rashin rarraba ayyuka a cikin sojoji

Manufofin tsaro na majalisar ministocin Isra'ila game da Gaza a cikin shekaru da suka gabata

Rashin tasirin Shin Bet wajen fuskantar Hamas

A baya dai sojojin Isra'ila sun buga wani rahoto kan kashin da suka sha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha