5 Disamba 2025 - 21:09
Source: ABNA24
Iran: IRGC Ta Gudanar Da atisayen Makamai Masu Linzami

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta gudanar da wani atisaye da ke kwaikwayon hare-haren makamai masu linzami da na jirgin ruwa don gwada yanayin basu umarni da ikonsu, dacewar na'urori masu aunawa firikwensin, da kuma daidaiton samun hadafi. Da manufar ƙarfafa kariya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma tabbatar da yanayin kare 'yancin ƙasa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Rundunar Sojojin Sama ta IRGC ta ruwaito cewa atisayen sun haɗa shirye-shiryen harba makamai, gano hadafi, da kuma bin diddigin hanyoyin da aka bi tare da kwaikwayon kimantawa bayan kai harin. Sassan sun tabbatar da daidaito tsakanin makamai masu linzami da na jirgin ruwa, gudanar da harba makamai masu linzami a jere, haɗa na'urorin radar da ke ƙasa da tsarin gani, da kuma ingancinsu ta sadarwa a cikin yanayin da ke cike da hayaki. Hukumomi ba su ƙayyade ainihin adadin harsasai masu rai da aka yi amfani da su a cikin atisayen ba, suna masu jaddada yanayin tsaronsu da aka tsara.

Wannan atisaye ya mayar da hankali kan tsara hadafofi masu motsi da nufarsu da tsarin makamin da ya dace da su.

Your Comment

You are replying to: .
captcha